Bayan Shekara 1 da Rasuwarsa, Hadimin Tinubu Ya Tuna Wata Matsala da Aka Samu a Mulkin Buhari

Bayan Shekara 1 da Rasuwarsa, Hadimin Tinubu Ya Tuna Wata Matsala da Aka Samu a Mulkin Buhari

  • Hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala ya tabo mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari bayan shekara guda da rasuwarsa
  • Bwala ya yi ikirarin cewa rashin hadin kan sojojin sama da na kasa a mulkin Buhari ya haifar da koma baya a yaki da matsalar tsaro
  • Ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta inganta hadin kai tsakanin hukumomin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Mai ba shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa, Daniel Bwala, ya tabo zamanin mulkin tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari.

Bwala ya yi zargin cewa rikicin da ya dabaibaye Rundunar Sojin Kasa da Rundunar Sojin Sama a zamanin Buhari ya janyo sojoji rasa tallafin sama a wasu ayyukan yaki.

Bwala.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Daniel Bwala Hoto: Daniel Bwala
Source: Facebook

Hadimin Tinubu ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin The Link Up Podcast, wanda EchoRoom ta shirya.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An cafke wasu yan ƙasashen waje kan zargin hannu a matsalar tsaron Najeriya

Bwala ya fadi matsalar mulkin Buhari

A cewarsa, an samu rashin jituwa tsakanin Babban Hafsan Sojin Sama da shugabannin Rundunar Sojin Kasa, lamarin da ya shafi hadin gwiwar da ake bukata a yayin gudanar da yyukan tsaro

Ya ce:

"Na tuna a zamanin Buhari cewa akwai sabani tsakanin Babban Hafsan Sojin Sama da shugaban Rundunar Sojin Kasa.
"Idan aka fara wani farmaki kuma aka nemi tallafin jiragen yaki, wasu lokuta ba a samun wannan tallafi. Amma a wannan gwamnati ta Tinububhakan ba ya faruwa, akwai hadin kai da aiki tare."

Ya musanta zargin sojoji na kare 'yan ta'adda

Bwala ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi kan zargin cewa kungiyoyin ta'addanci sun kutsa cikin rundunar sojin Najeriya.

Ya ce babu wata hujja da ke nuna cewa jami'an tsaro na kare 'yan ta'adda da gangan.

Ya ce:

"Ba na ganin haka. Wannan zato ne kawai, sai dai idan akwai takamaiman hujja da ta tabbatar da hakan."

Kara karanta wannan

Gwamnoni 6 sun shirya zuwa wurin Bola Tinubu kan tikitin musulmi da musulmi a zaben 2027

"Ba za ka iya cewa babu mutum daya ko biyu da ke ba su bayanai ba. An taba kama jami'an 'yan sanda, haka ma wasu jami'an tsaro da ke da hannu a irin wadannan laifuka."
Buhari.
Tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari Hoto: @MBuhari
Source: Twitter

Bwala ya ce irin wadannan matsaloli ba Najeriya kadai ke fuskanta ba, inda ya kawo misalin Edward Snowden, tsohon ma'aikacin da ke aiki da hukumomin leken asirin Amurka, wanda ya fallasa wasu sirrikan tsaro.

Ya ce gwamnati na daukar matakan dakile irin wadannan matsaloli, amma ba za ta bayyana dukkan dabarunta ba saboda dalilan tsaro, kamar yadd Vangurd ta ruwaito.

Bwala ya fadi nasarar sojojin Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kama wasu yan kasashen waje da ake zargi da hannu a rura wutar matsalar tsaro.

Mai ba shugaban kasa Bola Tinubu shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa, Daniel Bwala, ya ce ana zargin mutanen da haddasa matsalolin tsaro a wasu sassan Najeriya.

Bwala ya bayyana cewa rundunar soji ta ki bayyana kasashen da wadanda aka kama suka fito saboda dalilan tsaro da kuma ci gaba da tattaunawar diflomasiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262