Gwamna Ya Hana Ayyukan 'Hisbah' a Jiharsa, Ya ba Jami'an Tsaro Umarni

Gwamna Ya Hana Ayyukan 'Hisbah' a Jiharsa, Ya ba Jami'an Tsaro Umarni

  • Gwamna Caleb Mutfwang ya umarci a dakatar da ayyukan wata ƙungiya da ke aiki da sunan Hisbah a wasu sassan Jos ta Arewa
  • Gwamnan ya zargi ƙungiyar da tsoratarwa, cin zarafi, karɓar kuɗi ba bisa ka’ida ba da kuma sanya dokoki marasa izini
  • Mutfwang ya ce jami’an tsaro su gano tare da kama waɗanda ke da hannu, sannan a gurfanar da su idan an same su da laifi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau, ya bayar da umarnin dakatar da ayyukan wata ƙungiya da ake zargin tana gudanar da ayyuka da sunan Hisbah a wasu sassan ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.

Gwamnan ya bayyana ayyukan ƙungiyar a matsayin waɗanda ba su da izinin doka, ba su da tushe kuma ba za a amince da su ba.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta hango matsala, Ribadu ya yi gargadi kan barazanar tsaro a wasu wurare

Mutfwang ya hana ayyukan Hisbah
Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Harkokin Jama’a na gwamnan, Dr Gyang Bere, ya fitar ranar Lahadi, 30 ga watan Agustan 2026, cewar rahoton The Punch.

Umarnin ya biyo bayan rahotannin cewa ƙungiyar tana tsoratar da mazauna yankin, cin zarafinsu, karɓar kuɗi ba bisa ka’ida ba da kuma sanya wasu dokoki da ba hukumomin gwamnati suka amince da su ba.

Mutfwang ya yi gargadin kama masu hannu

Mutfwang ya gargadi duk mutanen da ke da hannu wajen ayyukan da su dakatar da su nan take, ko kuma su fuskanci kamawa da gurfanarwa bisa dokokin Najeriya.

Ya jaddada cewa Jihar Plateau tana da Kundin Tsarin Mulki guda ɗaya, tsarin doka guda ɗaya da kuma halastacciyar hukuma guda ɗaya, jaridar TheCable ta kawo labarin.

A cewarsa, babu wani mutum ko ƙungiya da ke da ikon karɓar wani nauyin da doka ba ta ba shi ba.

Kara karanta wannan

Sojoji sun rutsa yan ta'adda masu karɓar kudin fansa a jihar Kebbi

Gwamnan ya ce gwamnati ba za ta bari a samar da wata hukuma ta daban, ƙungiyar tilasta doka ta kai tsaye ko wata ƙungiya da za ta riƙa sanya wa jama’a dokoki, takunkumi ko hukunci ba tare da bin tsarin doka ba.

An umarci jami’an tsaro su gudanar da bincike

A cikin sanarwar, Gwamna Mutfwang ya ce babu wani mutum ko ƙungiya da ke da ikon ayyana kanta a matsayin gwamnatin Plateau.

“Alhakin tabbatar da bin doka yana hannun hukumomin da aka kafa bisa doka kuma suke aiki a cikin tsarin doka,” in ji shi.

Saboda haka, gwamnan ya umarci hukumomin tsaro a jihar da su gano, su kama tare da gudanar da bincike kan mutanen da ake zargi da hannu a ayyukan.

Ya ce idan bincike ya tabbatar da cewa sun aikata laifi, a gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar hukuncin da ya dace.

“Ba batun addini ko kabila ba ne”

Sai dai Mutfwang ya bayyana cewa umarnin ba ya nufin wata addini, ƙabila ko al’umma. Ya ce Plateau gida ne ga mutane masu addinai, ƙabilu da al’adu daban-daban, kuma kowa yana da haƙƙin samun kariya iri ɗaya a ƙarƙashin doka.

Kara karanta wannan

Amurka za ta janye sojojinta daga Najeriya, an sanya lokacin kwashe su

Gwamnan ya ce kowane mazaunin jihar yana da damar yin ibada, aiki, gudanar da kasuwanci na halal da kuma gudanar da harkokin rayuwarsa ba tare da wata ƙungiya ko hukuma ta kai kanta ta tsoratar da shi ko ta hana shi ba.

Gwamnan Plateau ya hana ayyukan Hisbah
Taswirar jihar Plateau, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Gwamna ya jaddada zaman lafiya

Mutfwang ya ce Plateau tana da tarihin zaman lafiya tsakanin mutane masu addinai, ƙabilu da al’adu daban-daban.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare wannan al’ada ta zaman lafiya ta hanyar tabbatar da tsaro, daidaita mu’amala da jama’a da kuma tabbatar da cewa bin doka shi ne mafi girman iko a jihar.

Batun Hisbah ta hana Kiristoci ibadah

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar Hisbah ta jihar Sokoto ta yi martani kan rahotannin da ke cewa ta sanya dokoki domin takaita yadda Kiristoci ke gudanar da ibadah.

Kwamandan hukumar Hisbah ta Sokoto, Dakta Usman Abdullahi Jatau, ya bayyana zarge-zargen a matsayin karya da yaudara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng