Gobara Ta Tashi a Gidan Gwamna Dauda Lawal na Zamfara

Gobara Ta Tashi a Gidan Gwamna Dauda Lawal na Zamfara

  • Gobara ta tashi a gidan Gwamnan Zamfara Dauda Lawal da ke GRA a Gusau da misalin karfe 7:20 na daren Talata, 1 ga watan Satumban 2026
  • Hukumar kashe gobara ta jihar ta tura jami’anta zuwa gidan gwamnan domin dakile gobarar tare da hana ta bazuwa zuwa wasu sassan gidan
  • Wata majiya ta ce gobarar ta shafi dakin tsaro, yayin da ba a bayyana musabbabin gobarar ko yawan barnar da ta haddasa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Gusau, Zamfara – An samu tashin gobara a gidan gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, da ke birnin Gusau.

Gobarar ta tashi ne a wani bangare na gidan Gwamna Dauda Lawal, da ke yankin GRA a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Gobara ta tashi a gidan Dauda Lawal
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:20 na daren Talata, 1 ga watan Satumban 2026 lamarin da ya sa jami’an hukumar kashe gobara ta jihar suka garzaya gidan gwamnan cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Najeriya ta tafka rashi, Allah ya yi wa mai martaba Sarkin Zurmi rasuwa

Jami’an kashe gobara sun isa gidan gwamnan

Shugaban Hukumar Kula da Kashe Gobara ta Zamfara, Injiniya Bello Sani Gusau, ne ya jagoranci tawagar jami’an hukumar zuwa gidan gwamnan domin shawo kan gobarar.

Da yake magana da jaridar yayin da jami’an ke kokarin kashe gobarar, Gusau ya tabbatar da faruwar lamarin.

“An samu gobara a gidan gwamnan, kuma a halin yanzu muna aiki domin shawo kanta.” In ji shi.

Gobarar ta shafi dakin tsaro

Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa gobarar ta shafi wani dakin tsaro da ke cikin gidan gwamnan.

Majiyar ta ce jami’an kashe gobara suna ci gaba da kokarin shawo kan gobarar tare da tabbatar da cewa ba ta bazu zuwa wasu sassan gidan ba.

Ba a gano musabbabin gobarar ba

A lokacin da ake hada wannan rahoto, ba a samu cikakken bayani kan musabbabin tashin gobarar ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari Kano, an sace babban mai rike da sarauta da kashe mutane

Haka kuma, ba a tabbatar da girman barnar da gobarar ta haddasa a gidan Gwamnan Dauda Lawal ba.

Ana sa ran hukumomin da abin ya shafa za su gudanar da bincike domin gano abin da ya haddasa tashin gobarar tare da tantance asarar da aka samu.

An samu tashin gobara a gidan gwamnan Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan jihar Zamfara

Gwamna Dauda ya yi ta'aziyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana matuƙar alhini bisa rasuwar Sarkin Zamfaran Zurmi, Mai Martaba Alhaji Bello Sulaiman.

Gwamnan ya ce mutuwar sarkin ba ta shafi iyalansa kaɗai ba, domin ta kasance babban rashi ga Masarautar Zurmi, cibiyar sarauta ta gargajiya da kuma daukacin al’ummar Jihar Zamfara.

Dauda Lawal ya ce Alhaji Bello Sulaiman zai kasance abin tunawa saboda irin hidimar da ya yi wa jama’arsa da kuma gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban masarautar gargajiyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng