'Neman Kudin Aure Ya Saka Ni Ta'addanci domin Faranta wa Mahaifiyata': Matashi

'Neman Kudin Aure Ya Saka Ni Ta'addanci domin Faranta wa Mahaifiyata': Matashi

  • ‘Yan sandan Lagos sun kama mutane uku da ake zargi da satar wata ’yar kasuwa, bayan sun karɓi N21m a matsayin kuɗin fansa
  • Ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya ce ya shiga aikin satar mutane tun 2010, amma ya koma cikinsa saboda neman kuɗi
  • Wani wanda ake zargin ya ce bukatar kuɗin aure ce ta sa ya shiga aikin satar mutane, inda ya samu N2.5m daga fansar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Mutanen da ake zargi da satar mutane sun fito ne daga ƙauyen Agadagba da ke ƙaramar hukumar Ese-Odo a Ondo.

Majiyoyi suka ce ba kasuwanci suka zo Lagos ba, kuma ba ziyara suka zo yi ba, sun zo ne domin satar mutane.

Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane a Lagos
Sufeta-janar na yan sanda, Rilwan Disu. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Yayin da ake karanta wannan rahoto, rundunar ’yan sandan Lagos ta kama wasu mutane uku da ake zargi da kasancewa cikin wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane da ke aiki a jihohi daban-daban, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun fatmaki mutane ana shirin yin sallah, an rasa rayukan bayin Allah

Zargin da ake yi wa mutane 3

Ana zargin su da sace wata ’yar kasuwa a yankin Ijedodo na Lagos, inda ta karɓi N21m a matsayin kuɗin fansa kafin sakin matar.

Waɗanda aka kama su ne Semi Buawe, mai shekaru 35; Oluwatomi Obosi, mai shekaru 37; da Bamure Telemowei.

Rundunar ’yan sandan ta ce jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane sun gano inda suke buya a ƙauyen Agadagba, ƙaramar hukumar Ese-Odo ta Ondo.

An ce shugabansu wanda aka bayyana da sunan ID kawai, ya tsere, yan sanda sun ce ana zarginsa da hannu a wasu ayyukan garkuwa da mutane a jihohi daban-daban.

An tsare wadda abin ya shafa na tsawon kwanaki uku a cikin daji da ke yankin Ijedodo, kafin iyalanta su biya kuɗin fansa.

Baya ga N21m, masu garkuwar sun kuma buƙaci kwalbar schnapps, 'power bank' da kilo ɗaya na kaza.

An kama masu garkuwa da mutane 3 a Lagos
Taswirar jihar Lagos da ke Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

'Soyayya ta jefa ni harkar garkuwa da mutane'

Kara karanta wannan

An shirya yadda za a yi garkuwa da Mbappe, shugaban Faransa ya yi magana

Ga Oluwatomi Obosi, mai shekaru 37, wanda aka fi sani da Tommy, ya ce burinsa na neman aure ne ya kai shi cikin harkar garkuwa da mutane.

Ya ce komai ya fara ne a watan Afrilu lokacin da yake tare da budurwarsa a gidansu da ke Ikorodu, cewar Daily Post.

Ya ce mahaifiyarsa ta gaya masa ya ɗauki batun soyayya da muhimmanci, ya zaɓi mace ya aure ta domin ya zama mai ɗaukar nauyi.

A cewarsa, kakansa ma ya ƙarfafa shawarar, inda ya umarce shi ya koma garinsu Agadagba a Ondo domin neman yarinya ta gari da kuma kuɗin gudanar da aure yadda ya kamata.

Tommy ya ce bayan ya koma Agadagba, ya samu wata yarinya ya nemi aurenta, sai dai yarinyar ta ce dole ne ya fara samun amincewar ’yar uwarta babba.

Ya ce:

“A lokacin ne aka haɗa ni da ID, wanda shi ne shugaban ƙungiyarmu. Shi ne mijin ’yar uwar budurwata, lokacin da ID ya gano cewa ina zaune a Lagos, ya gaya min shirin satar mutane.
"Ya ce yana son in riƙa fassara harshen Yoruba ga sauran ’yan ƙungiyar idan suka yi garkuwa da wanda yake magana da Yoruba, na amince in bi su ne kawai saboda ina buƙatar kuɗin yin aure cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An cafke likitoci, lauyoyi da masu ba 'yan bindiga bayanai

"Na samu N2.5m, wanda ya isa in fara sabuwar rayuwa. Amma lokacin da muka koma Agadagba, ID ya karɓi N200,000 daga kowannenmu.”

A yanzu, mutumin da ya ce kawai yana son faranta wa mahaifiyarsa rai da kuma cika burin kakansa na yin aure yana tsare a hannun ’yan sanda.

VeryDarkMan ya ba jami'an tsaro hakuri

An ji cewa dan gwagwarmaya a Najeriya, VeryDarkMan ya nemi afuwar sojoji, ’yan sanda, jami’an kwastam da shige da fice kan kalamansa.

Ya ce ya fahimci cewa kiran jami’an tsaro a taro ya lura bai dace ba, musamman ganin yadda suke sadaukar da rayukansu.

Mai fafutukar ya ce kalaman nasa ba su yi adalci ga jami’an da ke yaki da Boko Haram da sauran barazanar tsaro ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.