Dukkanku dajin Sambisa za ku garzaya, Buratai ga sojin da ake horarwa

Dukkanku dajin Sambisa za ku garzaya, Buratai ga sojin da ake horarwa

- Shugaban rundunar sojin kasan Najeriya, Tukur Buratai, ya ce sabbin soji su shirya tafiya Sambisa

- Ya sanar da hakan a ranar Litinin ga sojin da ake horarwa ne a dajin Falgore na jihar Kano

- Ya bukaci duk wani soja da bai shirya ba da ya kama hanyarsa ta zuwa gida domin ba za su amince da lalaci ba

Shugaban rundunar sojin kasan Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai a ranar Litinin ya sanar da sabbin kananan sojojin da ake horarwa cewa su shirya tafiya dajin Sambisa domin fuskantar 'yan ta'adda da sauran yankunan iyakokin kasar nan domin bata kariya, Daily Trust ta ruwaito.

Buratai, wanda yayi wannan jawabin yayin tantacewa ta karshe da ake wa sojojin a sansanin horarwa na dajin Falgore a jihar Kano, ya kara da cewa rundunar sojin Najeriya za ta jaddada tsantsaininta a wurin diban soji domin tabbatar da an dauka wadanda suka dace.

Dukkanku dajin Sambisa za ku garzaya, Buratai ga sojin da ake horarwa
Dukkanku dajin Sambisa za ku garzaya, Buratai ga sojin da ake horarwa. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kai wa Sanata hari a Osun yayin taro a mazaɓarsa

Shugaban sojin ya yi kira garesu da su hakura da aikin idan har basu shirya zama masu biyayya tare da zuwa duk inda aka turasu ba domin hakan sabuwar hanya ce ta tanntacewa ta rundunar sojin.

Kamar yadda yace, wannan atisayen ana yin shi ne saboda tsabar bukatar jajirtattun sojoji da za su iya shiga duk inda ake so.

"Rundunar sojin Najeriya bata shiryawa lalaci ba, saboda haka dole ku saka a zuciyarku cewa za ku bautawa kasar ku ne a matsayin sojoji. Ku shirya cewa za a iya tura ku ko ina. Dukkanku Sambisa za a tura ku bayan kun gama karbar horarwar da ta dace.

KU KARANTA: Gobara ta kashe mutane uku a Kano

"Idan baku shirya zuwa Sambisa ba da sauran wuraren don bai wa kasar ku kariya, toh ku dage yanzu.

"Amma kuma har yanzu baku makara ba, idan akwai wanda yake da tantama, zai iya ajiye kayansa ya kama hanya. Ba za mu lamunci lalaci ba," Shugaban ya tabbatar.

Ya kara da jaddada cewa dukkan wani horarwa ko tamtancewa daga yanzu za a dinga yin shi ne a dajin Falgore.

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel