Kamfanin Opay Ya Nemi Agajin DSS, Ƴan Sanda kan Jita Jitar Zai Gudu a Najeriya
- Kamfanin OPay ya bukaci DSS da ’yan sanda su binciki jita-jitar ƙarya cewa yana shirin dakatar da ayyukansa a Najeriya daga ranar 1 ga Satumba
- OPay ya ce jita-jitar na iya haddasa firgici, asarar kuɗi da kawo cikas ga tsarin kuɗaɗen Najeriya, don haka jami’an tsaro suka fara bincike
- Kamfanin ya tabbatar da cewa yana ci gaba da gudanar da ayyukansa yadda ya kamata, ya gargadi jama’a da su tabbatar da sahihancin bayanai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kamfanin fasahar kuɗi na OPay ya ce ya nemi agajin Sashen Tsaro na Farin Kaya (DSS) da ’Yan Sandan Najeriya.
Kamfanin ya bukaci su binciki bayanan ƙarya da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa kamfanin yana shirin rufewa.

Source: Facebook
Martanin Opay kan jita-jitar guduwa
Babban Lauyan OPay, Akinfolabi Rokosu, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Lagos ranar Laraba, cewar Nairametrics.
Ya ce kamfanin ya shigar da jami’an tsaro saboda jita-jitar na iya kawo cikas ga tsarin kuɗaɗen Najeriya da jawo asarar kuɗi.
Matakin OPay na neman a gudanar da bincike ya biyo bayan wani saƙo da ya bazu sosai a ranar Lahadi, wanda ya bukaci kwastomomi su cire kuɗaɗensu saboda zargin cewa kamfanin zai dakatar da ayyukansa daga ranar 1 ga Satumba.
Abin da OPay ke cewa
Rokosu ya jaddada cewa OPay ba ya shirin dakatar da ayyukansa, kuma yana ci gaba da gudanar da harkokinsa a Najeriya yadda ya kamata. Ya ce za a hukunta duk waɗanda aka samu da hannu wajen yaɗa labarin ƙaryar.
Ya ce:
ayin da DSS da ’yan sandan Najeriya, tare da sauran hukumomin tsaro da abin ya shafa, ke gudanar da bincike mai zurfi kan wannan batu, muna ba da cikakken haɗin kai ga binciken da ake gudanarwa, kuma mun samar da hujjojin da suka dace domin gano waɗanda ke da hannu a ciki.
"Opay na ɗaukar mataki kan waɗanda suka ƙirƙira da yaɗa wannan bayani mai cutarwa. Za mu bi diddiginsu kuma za mu tabbatar da cewa an aiwatar da doka yadda ya kamata.
"Duk wanda da gangan ya shiga irin wannan aiki ya kamata ya sa ran ɗaukar matakin shari’a mai tsauri da fuskantar dukkan hukuncin da doka ta tanada. Wannan ba batun hana kowa magana ba ne. OPay ba zai yi shiru ba.”
Shi ma Babban Jami’in Gudanarwa kuma Babban Jami’in Fasaha na OPay, Dotun Adekunle, ya shawarci ’yan Najeriya da kada su ɗauki wani matakin kuɗi bisa saƙonnin da aka wallafa a kafafen sada zumunta ko manhajojin aika saƙonni ba tare da tabbatar da tushensu ba.
Ya ce:
"Sako na iya zama kamar na hukuma amma ya kasance ƙarya tsantsa. Ana iya kwafar tambari. Ana iya tsara takarda ta yadda za ta yi kama da sahihiya.
"Ko da mutane 200,000 sun yaɗa shi, har yanzu bayanin ƙarya ne. Yawan mutanen da ke bayyana ƙarya ba ya mayar da ƙarya gaskiya. Ƙarya tana nan a matsayin ƙarya.”
Matsayar CBN kan jita-jita kan Opay
Adekunle ya ce OPay na ci gaba da gudanar da ayyukansa ba tare da wata matsala ba. Ya ƙara da cewa Babban Bankin Najeriya (CBN), wanda shi ne babban mai kula da harkokin kuɗi a ƙasar, shi ma ya shiga batun domin karyata jita-jitar.
Ya ce wannan ya nuna irin muhimmancin batun da kuma dalilin da ya sa ya kamata ’yan Najeriya su yi watsi da duk wani saƙo da ke nuna cewa OPay zai daina aiki.
Opay ya magantu kan jita-jitar guduwa
An ji cewa kamfanin hada-hadar kudi na OPay ya karyata rahotannin da ke cewa zai dakatar da ayyukansa daga ranar Talata, 1 ga Satumba, 2026.
Kamfanin ya ce babu wani shiri na dakatar da ayyukansa, yana mai tabbatar wa kwastomomi cewa za su ci gaba da amfani da ayyukansa.
OPay ya bukaci jama’a su rika tantance sahihancin bayanai kafin su yada su, musamman idan sun shafi kudade ko asusun banki.
Asali: Legit.ng


