Yan Bindiga Sun Shiga Garuruwa 17, Sun Halaka Bayin Allah da har Yanzu ba Gano Yawansu
- Akalla kauyuka 17 a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina sun fuskanci hare-haren ’yan bindiga tun ranar Juma’a da ta gabata
- Hare-haren sun jefa mazauna yankin cikin fargaba, yayin da wasu iyalai suka tsere daga gidajensu saboda tsoron rasa rayukansu
- Kungiyar kare hakkin dan adam ta bukaci gwamnati ta kara daukar matakan tsaro tare da kokarin kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Akalla kauyuka 17 da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina ne aka ruwaito cewa ’yan bindiga sun kai wa hare-hare tun daga ranar Juma’a zuwa karshen mako.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kashe mazauna wasu kauyuka da a tantance yawansu ba tare da yin garkuwa da wasu da dama.

Source: Original
Leadership ta rahoto cewa hare-haren sun jefa mazauna yankin cikin fargaba, yayin da aka ce wasu sun tsere daga gidajensu saboda damuwa kan tsaron rayukansu.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun sauke fushin abin da jami'an tsaro suka masu kan manoma a Sakkwato
An kai hari kauyuka 17 a jihar Katsina
A cewar rahoton da kungiyar hakkin da adam ta Nigerian Human Rights Protection and Initiative reshen Faskari ya fitar, maharan sun kuma wawushe dukiyoyin mazauna yankin yayin hare-haren.
Shugaban kungiyar na karamar hukumar, Shamsudeen Sulaiman, ya bayyana cewa ’yan bindigar sun tafi da dabbobin gida da na kiwo, lamarin da ya kara ta’azzara asarar tattalin arzikin mazauna yankin
“An kai wa kauyuka 17 hare-hare,” in ji kungiyar, inda ta kara da cewa hare-haren sun yi sanadin asarar rayuka da sace mutane.
An bukaci gwamnati ta dauki mataki
Kungiyar ta yi kira da a dauki matakan tsaro cikin gaggawa tare da karfafa jami’an tsaro domin kare mazauna yankin da kuma hana sake aukuwar hare-hare.
Kungiyar ta kuma roki hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen ganin an kubutar da mutanen da maharan suka yi garkuwa da su.
Haka kuma, wani jami’in gwamnati wanda yake mazaunin Faskari ya tabbatar da faruwar lamarin yayin wata tattaunawa ta wayar tarho, inda ya bayyana hare-haren a matsayin ramuwar gayya.
Ana zargin harin ramuwar gayya ne
Ya ce lamarin ya biyo bayan wasu sojoji daga jihar Zamfara da ake zargin sun kama wasu Fulani da ke dawowa daga kasuwar Laraba a yankin Yankara.
A cewar jami’in, sojojin sun zargi wasu daga cikin Fulani da aka kama da hannu wajen hare-haren ’yan bindiga da aka kai a jihar Zamfara a baya-bayan nan.

Source: Twitter
Jami’in ya kara da cewa tun bayan faruwar lamarin ranar Larabar makon da ya gabata, kauyukan Faskari sun fuskanci sake tabarbarewar tsaro, ciki har da hare-hare, kashe-kashe da sace mutane.
A lokacin hada wannan rahoto, rundunar ’yan sandan jihar Katsina ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan sababbin hare-haren da ake zargin an kai a karamar hukumar Faskari ba.
Yan bindiga sun kashe manoma 8
Kun ji cewa wasu miyagun ’yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan manoman kauyen Ghandi da ke karamar hukumar Rabah ta jihar Sokoto.
Akalla manoma takwas ne aka kashe, yayin da wasu biyar suka samu raunukan harbin bindiga bayan yan bindigar sun bude masu wuta kan mai uwa da wabi.
Asali: Legit.ng
