Hana bara a Kano: Halin da almajirai suka shiga

Hana bara a Kano: Halin da almajirai suka shiga

A wata bola da ke kan titin Kotu a Gyadi-Gyadi da ke birnin Kano, wakilin jaridar Daily Trust ya hadu da wani amajiri mai suna Auwal Mohammed Auwal wanda bai wuce shekaru 12 ba a duniya.

Ya ce, "Tunda gwamnatin jiha ta hana mu yin bara a tituna, wannan ne kadai abinda zamu iya yi. Muna duba bolar ne don samun duk abinda zai iya amfanarmu na daga abinci ko sutura. Wasu daga cikinmu kan samu sutura, takalma ko abinci a nan."

Ya kara da bayyana cewa, tun bayan da gwamnatin jihar Kano ta haramta bara a titunanta, da yawansu suna samun matsala wajen cin abinci ballantana kananan. Ya ce da yawansu basu iya sana'o'in da zasu kawo musu kudi ba a halin yanzu.

A ranar Talatar da ta gabata ne gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana haramta bara a titunan jihar. Ta kara da cewa duk mahaifin da aka kama dan sa na yawon bara a jihar, tabbas zai fuskanci fushin hukuma.

Amma kuma yayin karin bayani, Sakataren yada labarai na gwamnan, Abba Anwar ya ce akwai banbanci tsakanin sanar da doka da kuma tabbatar da ita. Ya ce abinda ya faru a filin wasa na Sani Abacha din a ranar Talata shi ake kira da sanar da doka.

Anwar ya bayyana cewa, gwamnan ya sanar da dokar ne amma duk tsarikan da zasu sa dokar ta tafi yadda ake so suna kan hanya.

Hana bara a Kano: Halin da almajirai suka shiga
Hana bara a Kano: Halin da almajirai suka shiga
Source: UGC

DUBA WANNAN: Hargitsi tsakanin shugabannin Boko Haram da ISWAP: Akwai yuwuwar Shekau ya sheka lahira

Zancen barar almajirai a titunan jihar Kano ya dade yana cin tuwo a kwaryar gwamnatocin jihar da suka shude. Gwamnati daban-daban ta yi kokarin ganin ta hana tare da dakile wannan dabi'ar ta bara a titunan jihar.

Idan za a tuna, tsarin karatun Islamiyah da na Tsangaya an hade su da karatun boko inda aka kirkiro da shirin ciyar da daliban ta yadda za a rage yawan almajiran da ke yawo a kan titunan jihar Kano.

A 2016 ne gwamnatin jihar Kano din ta ware N150m daga cikin kasafin kudinta don saka shi cikin hadadden tsarin na makarantun islamiyah da tsangaya a jihar.

Kamara dai yadda shugaban majalisar kolin malaman jihar Kano din, Sheikh Ibraheem Khalil ya bayyana, gwamnatin tayi gaggawar zartar da wannan hukuncin ta yadda ba ta tuntubi masu ruwa da tsaki ba ko kuma Malaman makarantun don gano tushen matsalar da matakan da ya dace a dauka ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel