Kano: Rundunar 'yan sanda ta kama kwararrun barayin mota hudu, sunayensu
- Rundunar 'yan sanda a Jihar Kano ta kama wasu matasa hudu da suka kware wajen satar mota
- Matasan hudu, mazauna unguwar Sheka, sun tsallaka gidan wani mutum Abba Adam tare da sace motarsa bayan sun raunata matarsa
Rundunar 'yan sandan Nigeria reshen jihar Kano ta sanar da cewa ta gano tare da samun nasarar cafke wata tawagar barayin mota.
Rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa ta bankado asirin tawagar barayin su hudu bayan kama daya daga cikinsu mai suna Al'amin Mohammed Bello, dan shekara 20, kamar yadda HumAngle ta rawaito.
A cewar Abdullahi Haruna Kiyawa, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, jami'an rundunar Puff Adder a karkashin jagorancin CSP Musa Umar, sune suka kama matashin.
Kiyawa ya bayyana cewa an kama matashin ne yayin da yake kokarin sayar da wata motar sata.
KARANTA: An fara gulma da tsegumi bayan fadar shugaban kasa da gwamna Zulum sun yi gum a kan ganawarsu
Kakakin ya kara da cewa matashin ya bayyana sunayen sauran abokansa da suka hada da Yusuf Lawan; mai shekaru 21, Abubakar Hassan; mai shekaru 28, da Yahaya Salisu; mai shekaru 28.
Kazalika, Kiyawa ya bayyana cewa matasan sun saci motar ne bayan sun balle gidan wani mutum mai suna Abba Adam.
KARANTA: Katsina: 'Yan bindiga sun koma cikin fushi bayan guduwar mutane 8 da suka sace, sun sake sace wasu 9
Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa Abba ya shigar da korafin cewa wasu batagari sun shiga gidansa sun raunata matarsa tare da sace motarsa.
Kiyawa ya sanar da cewa an garzaya da matar Abba zuwa asibiti yayin da su kuma barayin za'a gurfanar da su da zarar an kammala bincike.
Legit.ng ta rawaito cewa tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya yi kira ga 'yan Najeriya tare da kalubalantar Buhari da shugabanni akan su daina dorawa Allah laifin rashin cigaban kasa.
Obasanjo ya bayar da wannan shawara ne a dakin karatunsa mai suna Olusegun Obasanjo Presidential Library dake Abeoluta cikin jihar Ogun a wani sakonsa na shiga sabuwar shekara.
Ya kalubalanci shugaba Buhari da sauran shugabanni su daina dora alhakin halin da Najeriya ke ciki kan Ubangiji, su zargi kansu kurum.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng