Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya za ta yaye Dalibai 8, 260 a bana

Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya za ta yaye Dalibai 8, 260 a bana

- Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya za ta yaye ‘Dalibai sama da 8,000

- Daga ciki akwai sama da 250 da su ka samu takardar PHD na Dakta

- Shugaban Jami’ar Farfesa Ibrahim Garba ya bayyana wannan jiya

Yanzu haka an samu labari cewa babbar Jami’ar nan ta Najeriya tana yaye Daliban ta inda sama da mutane 8,000 za su karbi takardar shaidar kammala Digiri.

Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya za ta yaye Dalibai sama da 8, 200
Babbar Jami’ar Najeriya tana yaye Daliban 8260

Kamar yadda labari yake zuwa mana, Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya za ta yaye Dalibai 8, 260 a karshen makon nan. Daga cikin masu kammala karatun akwai har Dalibai akalla 256 da za su samu shaidar Digiri na 3 watau PhD daga Jami’ar.

KU KARANTA: Wani Dan Arewacin Najeriya ya ciri tuta a harkar rubuce-rubuce

Shugaban Jami’ar Farfesa Ibrahim Garba ya zanta da manema labarai kafin yau inda ya tabbatar da wannan yana mai cewa hakan ya nuna Jami’ar da gaske ta ke wajen karatun Digiri na biyu da ma na uku watau PhD na zama Dakta.

Yanzu haka dai Jami’ar na kara daukar ‘Dalibai fiye da da kuma ana kara fadada Makarantar da yawan kwas-kwasan da ake yi. Har wa yau Jami’ar na kara hada kai da wasu Makarantu. Kaf Yammacin Afrika babu katafariyar Makaranta irin ABU Zaria.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng