IPOB Ta Yi Barazanar da za Ta Shafi Zaben 2027 kan Nnamdi Kanu

IPOB Ta Yi Barazanar da za Ta Shafi Zaben 2027 kan Nnamdi Kanu

  • Ƙungiyar IPOB ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 14 domin tabbatar da cewa an saurari ɗaukaka ƙarar da Nnamdi Kanu ya shigar
  • IPOB ta yi barazanar cewa idan ba a saurari ƙarar cikin wa’adin ba, za ta ayyana cikakken kaurace wa zaɓukan da za su gudana a 2027
  • Ƙungiyar ta kuma yi tambaya kan tushen dokar da aka yi amfani da ita wajen samun Kanu da laifi da kuma ci gaba da tsare shi a kurkuku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ƙungiyar IPOB ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 14 domin tabbatar da cewa an saurari ɗaukaka ƙarar da shugaban ƙungiyar, Nnamdi Kanu, ya shigar kan hukuncin da aka yanke masa.

Ƙungiyar ta yi barazanar cewa za ta yi kira ga magoya bayanta da su kaurace wa dukkan zaɓukan da za su gudana a Biafra da sauran wurare idan gwamnati ta gaza cika buƙatarta cikin wa’adin da ta kayyade.

Kara karanta wannan

2027: 'Yan adawa sun kafa kwamitin fitar da tsarin kayar da APC a kwana 30

Nnamdi Kanu a kotu
Lokacin da aka yi wa Nnamdi Kanu shari'a a kotu. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Twitter

IPOB ta soki jinkirin shari'ar Kanu

Rahoton Vaguard ya nuna cewa IPOB ta bayyana matsayarta ne a cikin wata sanarwa da kakakinta, Emma Powerful, ya fitar ranar Talata.

Ƙungiyar ta zargi gwamnatin tarayya da gaggauta gurfanar da Kanu da kuma samun hukuncin daurin sa, amma ta ce gwamnati ba ta nuna irin wannan gaggawar wajen mayar da martani ga ɗaukaka ƙarar da aka shigar ba.

IPOB ta kuma yi tambaya kan tushen dokar da aka yi amfani da ita wajen samun Kanu da laifi da kuma ci gaba da tsare shi, tana neman a bayyana takamaiman laifin da ya sa ake ci gaba da tsare shi.

An ce akwai wata ƙara a kotu

Ƙungiyar ta ce baya ga ɗaukaka ƙarar, akwai wata ƙara da ke gaban Kotun Ƙoli da ta shafi halaccin ci gaba da shari’ar Kanu bayan an soke wasu daga cikin tuhume-tuhumen da aka yi masa a baya.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan hukumar EFCC 40 sun jawo wa kansu matsala a wurin aiki

A cewar IPOB, dole gwamnatin tarayya ta kare hukuncin da aka yanke wa Kanu tare da bayyana tushen ikon kotun da aka dogara da shi wajen ci gaba da shari’ar.

Nnamdu Kanu kafin a kama shi
Jagoran IPOB da ke zaman kurkuku. Hoto: Omoyele Sowore
Source: UGC

Zabin IPOB ga gwamnati

Rahoton PM News ya nuna cewa IPOB ta ce gwamnatin tarayya na da zaɓi biyu kawai kan batun Nnamdi Kanu.

Ta ce ko dai gwamnati ta sake Kanu nan take ba tare da wani sharaɗi ba, ko kuma ta bayyana a gaban kotu domin kare hukuncin da aka yanke masa da kuma tushen doka da aka yi amfani da shi wajen gudanar da shari’ar.

Ƙungiyar ta sake jaddada buƙatarta ta a saki Kanu nan take kuma ba tare da wani sharaɗi ba.

Sylva ya fice daga APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon Gwamnan Bayelsa kuma tsohon ministan mai, Timipre Sylva, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC.

Sylva ya kuma soki gwamnatin shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ta ba wa mafi yawan ’yan Najeriya kunya, tare da bayyana kwarin gwiwarsa cewa za a kawo sauyi a 2027.

A cikin wasiƙar murabus ɗinsa mai kwanan wata 31 ga Agusta, 2026, Sylva ya ce ba zai iya ci gaba da zama cikin jam’iyyar da shugabanninta suka rungumi hanya maras kyau ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng