FG ta buɗe sabon shafin yanar gizo, ta ƙirƙiri manhajar wayar hannu - Pantami

FG ta buɗe sabon shafin yanar gizo, ta ƙirƙiri manhajar wayar hannu - Pantami

- Gwamnatin tarayya ta kaddamar da sabon shafin yanar gizo tare da manhajar wayar hannu, domin bunkasa tattalin arziki ta kafar yanar gizo

- Dr. Isa Pantami, ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani (FMCDE) ya kaddamar da shafin tare da manhajar mai suna 'Digital Nigeria'

- Pantami ya bunkaci 'yan Nigeria da su yi rejista a wadannan shafukan; https://digitalnigeria.gov.ng; da kuma https://academy.nitda.gov.ng/

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da sabon shafin yanar gizo tare da manhajar wayar hannu, a shirin mayar da ayyukan gwamnatin Nigeria a tsarin yanar gizo.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da wannan shiri na Nigeria a yanar gizo (DNP) a ranar 19 ga watan Maris, 2020.

Dr. Isa Pantami, ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani (FMCDE) ya kaddamar da shafin tare da manhajar a ranar Litinin, ta hanyar bidiyo a yanar gizo, a birnin tarayya Abuja.

KARANTA WANNAN: Munafukai daga cikin mukarrabanka ne ke jawo maka zagi - Shawarar Okorocha ga Buhari

FG ta buɗe sabon shafin yanar gizo, ta ƙirƙiri manhajar wayar hannu - Pantami
FG ta buɗe sabon shafin yanar gizo, ta ƙirƙiri manhajar wayar hannu - Pantami - @GuardianNigeria
Asali: Twitter

Pantami ya ce wannan na daga cikin yunkurin gwamnati na bunkasa masu kirkira da kasuwanci na zamani, ta hanyar ilimantar da su kan yin harkalloli ta yanar gizo don samun kudi.

Ya bayyana cewa shirin Nigeria a yanar gizo na daga cikin shiri da tsarin gwamnati na daga dajarar tattalin arziki ta hanyar yanar gizo, wanda shi ya kaddamar da shirin.

KARANTA WANNAN: Majalisar Dinkin Duniya na son a yafe wa wanda da ya yi batanci ga Annabi a Kano

Pantami ya ce ma'aikatar na hadaka da cibiyoyin kasashen waje da suka hada da bankin bunkasa Afrika (AFDB) da kuma kamfanin Microsoft, domin ganin 'yan Nigeria na cin moriyar yanar gizo a cikin gidajensu.

Sai dai Ministan, ya ce gwamnati za ta fi mayar da hankali kan bunkasa mutanen da suke da basirar kasuwanci ta yanar gizo, ba wai la'akari da takardun da mutum ya mallaka ba.

"Muna kokarin ganin cewa mun mayar da hankali kan kwarewa da fasaha, ba zamu yi la'akari da takardun karatu ba, ma damar ba ka da fasaha da kwarewa, ba zamu bunkasa ka ba.

"Ana amfani da takardun Degree ne kawai don daga darajar fasaha da kwarewa, amma abunda aka fi mayar da hankali akanshi a fadin duniya, shine kwarewar mutum da fasaharsa.

"Wannan shirin zai taimaka ainun wajen kara horaswa da kuma bunkasa mutanen da ke da kwarewa da fasahar amfani da yanar gizo, don ci gaban tattalin arziki.

"Digital Nigeria" manhajar wayar hannu na a rumbun PlayStore da Apple Store, wanda zai baiwa 'yan Nigeria damar shiga darussa na kimiyar yanar gizo, su koyi karatu a gidajensu," a cewar sa.

Pantami ya bunkaci 'yan Nigeria da su amfani da wannan damar wajen yi wa kawunansu rejista a wadannan shafukan; https://digitalnigeria.gov.ng; da kuma https://academy.nitda.gov.ng/

"Shafukan za su bayar da cikakken bayani yadda za ayi rejista da kuma sauke manhajar da ta dace.

"Za mu ci gaba da sabunta darussan domin su dace da zamani. Shirin Digital Nigeria zai samar da muhallin da 'yan Nigeria za su bunkasa iliminsu kan na'ura mai kwakwalwa da yanar gizo."

Wasu daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da Farfesa Umar Danbatta, mataimakin shugaban hukumar NCC, da kuma Farfesa Mohammed Abubakar, shugaban kamfanin Galaxy Backbone (GBB).

A wani labarin, Tsohon gwamnan jihar Imo, kuma Sanata mai wakiltar Imo ta Yamma, Rochas Okorocha ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauki kwakkwaran mataki kan hadimansa.

Rochas Okorocha, ya shawarci shugaban kasar, kan mukarrabansa da ba sa tsinana komai a bangarorin da aka nada su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel