Dalilin ICPC na Tsame Sunan Gbajabiamila daga Kafa Hukumar PFIPC
- ICPC ta kammala binciken ta game da zargin Femi Gbajabiamila da nadin Adeniyi Adeyemi a matsayin shugaban wata hukumar bogi
- Binciken ya nuna cewa Adeyemi ne ya ƙirƙiri takardar nadin kansa tare da amfani da takardar kai ta fadar shugaban ƙasa da sa hannun Gbajabiamila.
- Hukumar ta ce gazawar wasu hukumomin gwamnati wajen tantance sahihancin takardu ya taimaka wajen kafa hukumar bogi ta PFIPC a kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
PFIPC – Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta (ICPC) ta ce ba ta gano wata hujja da ke nuna cewa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya san da zaman PFIPC ba.
ICPC ta ce babu alakar Gbajabiamila da naɗa Adeniyi Adeyemi a matsayin Darakta-Janar na hukumar bogi ta PFIPC da aka kirkira ta haramtacciyar hanya.

Source: Twitter
Premium Times ta kawo labarin cewa ICPC ta bayyana PFIPC a matsayin wata cibiya da ba a kafa ta bisa doka ba, yayin da bincikenta ya nuna cewa Adeyemi ne da kansa ya nada kansa a watan Maris na 2024.
Sakamakon binciken ICPC kan Gbajabiamila
Binciken ICPC ya ce an yi amfani da takardar kai ta bogi mai kama da ta Fadar Shugaban Ƙasa wajen ƙirƙirar takardar, sannan aka jingina sa hannun Gbajabiamila a kanta.
Binciken ya kuma nuna cewa babu wata hujja da ke tabbatar da cewa Gbajabiamila ya naɗa Adeyemi ko kuma ya taɓa yin wata mu'amala kai tsaye da shi.
A cewar ICPC, ba a samu wata alaƙa tsakanin Gbajabiamila, ofishinsa ko Fadar Shugaban Ƙasa da Adeyemi, PFIPC ko wani mutum da ke wakiltar wannan cibiya ba.
Shugaban hukumar bogi ya kira ruwa
A wani rahoton wucin-gadi da hukumar ta miƙa wa shugaban ƙasa ranar 6 ga Agusta, 2026 wanda aka samu kwafinsa, ICPC ta ce Adeyemi bai taɓa samun naɗin aiki daga gwamnatin tarayya ba.

Source: Facebook
Binciken ya kara da cewa sannan babu wata doka, umarnin shugaban ƙasa ko wata takardar gwamnati ingantacciya da ta kafa PFIPC.
Saboda haka, hukumar ta ba da shawarar a gurfanar da Adeyemi bisa zargin ƙirƙirar takardu, kwaikwayon mutum da sauran laifukan da suka shafi lamarin.
ICPC ta gano cewa Ofishin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa ba ya bayar da takardun naɗin masu riƙe da muƙaman siyasa ko shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati.
ICPC ta gano gazawar ofishin kasafin kudi
Kun ji a baya cewa hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta ce Ofishin Kasafin Kuɗi bai tantance sahihancin hukumar PFIPC ba kafin shigar da ita cikin kasafin 2026.
PFIPC da aka tabbatar da cewa hukumar bogi ta PFIPC ce ta nemi N3.85bn, amma daga baya aka ware mata Naira biliyan 1.3 a kasafin kuɗin tarayya na 2026.
Hukumar ICPC mai yaki da rashawa a Najeriya ta bayyana cewa ba ta gano shaidar cewa an saki ko kashe N1.3bn da aka ware wa hukumar ba PFIPC ba.
Asali: Legit.ng

