Da Gaske Opay Zai Daina Aiki kuma Yan Najeriya Za Su Rasa Kudadensu? Gaskiya Ta Fito
- Kamfanin hada-hadar kudi na OPay ya karyata rahotannin da ke cewa zai dakatar da ayyukansa daga ranar Talata, 1 ga Satumba, 2026
- Kamfanin ya ce babu wani shiri na dakatar da ayyukansa, yana mai tabbatar wa kwastomomi cewa za su ci gaba da amfani da ayyukansa
- OPay ya bukaci jama’a su rika tantance sahihancin bayanai kafin su yada su, musamman idan sun shafi kudade ko asusun banki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Wata jita-jita da ta yadu a kafafen sada zumunta ta yi ikirarin cewa kamfanin fasahar hada-hadar kudi na Opay zai dakatar da ayyukansa na wani lokaci ba tare da kayyade lokacin komawa ba.
Rahoton ya kuma bukaci masu amfani da OPay su cire kudaden da ke cikin asusunsu gabanin lokacin da aka ce kamfanin zai rufe ayyukansa, lamarin da ya haifar da fargaba.

Source: UGC
Da gaske Opay zai dakatar da aiki?
A wata sanarwa da ya wallafa a shafin X, kamfanin hada-hadar kudade ta yanar gizo, OPay, ya karyata rahotannin da ke cewa zai dakatar da ayyukansa daga Talata, 1 ga Satumba, 2026.
OPay ya bayyana jita-jitar a matsayin karya da kuma wani yunkuri na bata suna, inda ya tabbatar wa abokan huldarsa cewa ba shi da wani shirin dakatar da ayyukansa a Najeriya.
“OPay ba zai tafi hutu a watan Satumba ba. Muna nan, kuma babu inda za mu je!” in ji kamfanin a wani sako da ya wallafa a kafafen sada zumunta ranar Lahadi.
Opay ya ja hankalin mutane
Kamfanin ya kuma gargadi abokan huldarsa da su yi taka-tsantsan da bayanan da ba na hukuma ba da ke yawo a intanet, yana mai cewa ana iya bambance sahihan sakonnin kamfanin da na bogi.
“Masu amfani da OPay na gaskiya sun san yadda za su gane sakonninmu. Ku kara duba sakon da ke yaduwa, za ku ga alamun da ke nuna cewa ba gaskiya ba ne,” in ji shi.
OPay ya shawarci jama’a da su tabbatar da sahihancin bayanai kafin su yada su, musamman idan irin wadannan ikirari sun shafi kudadensu ko asusunsu.
Kamfanin ya kara da cewa, “Koyaushe ku tabbatar da sahihancin bayani kafin ku yada shi. Ku tace farfagand.”

Source: Getty Images
Ya kuma bukaci kwastomomi da su rika amfani da sahihan shafukansa na kafafen sada zumunta domin samun sabsbbin bayanai da sauran sanarwar hukuma.
Wannan karin bayani na OPay ya zo ne a daidai lokacin da ake kara nuna damuwa kan yadda bayanan karya ke yaduwa a kafafen sada zumunta, inda kamfanin ke gargadin kwastomominsa da kada su dauki mataki bisa ikirarin da ba a tabbatar ba.
An yi wa bankin Zenith kutse
A wani labarin, kun ji cewa rahotanni sun nuna cewa wasu masu kutsen yanar gizo sun kai hari kan bayanan Zenith Bank, daya daga manyan bankunan Najeriya.
Bankin ya ce masu kutsen sun samu bayanan wasu abokan hulda da ke da asusu, wanda suka hada da imel da lambobin waya
Sai dai bankin ya jaddada cewa lamarin bai shafi manyan bayanan sirri ko ayyukansa ba, yana mai cewa hanyoyin hada-hadar kudi da na’urorin sadarwa na zamani suna ci gaba da aiki yadda ya kamata.
Asali: Legit.ng

