Mazauna Kwaryar Gombe Sun Shiga Jimami da Aka Sanar da Mutuwar Sarki

Mazauna Kwaryar Gombe Sun Shiga Jimami da Aka Sanar da Mutuwar Sarki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa Allah Ya yi wa Hakimin Bolari, Alhaji Ahmad Abubakar, rasuwa cikin daren Juma'a
  • Rasuwarsa ta jefa al’ummar Bolari da sauran jama’ar Gombe cikin alhini da jimami, yayin da ake ta addu’o’i ga marigayin
  • Ana roƙon Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya jiƙansa da rahama, Ya sanya Aljannar Firdausi makomarsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Mun samu labarin rasuwar basarake a birnin Gombe wanda aka tabbatar da cewa ya rasu bayan fama da jinya.

Majiyoyi suka ce Hakimin Bolari da ke kwaryar Gombe, Alhaji Ahmad Abubakar ya rasu cikin daren Juma'a 28 ga watan Agustan shekarar 2026.

Hakimin Bolari a Gombe a rasu
Marigayi Hakimin Bolari a Gombe, Alhaji Ahmad Abubakar. Hoto: Hassan Saleh.
Source: Facebook

Rahoton Gombawa wanda wakilin Legit Hausa ya bibiya a shafin Facebook ya ce marigayin ya rasu bayan fama da wani yanayi na rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Fin karfi: Ana zargin Kwamishina ya raba aure, ya lallaba ya auri matar a Zamfara

Hakimin Bolari ya rasu a Gombe

Rasuwar marigayin ta jefa al’ummar Bolari da sauran jama’ar Jihar Gombe cikin babban alhini da jimami, yayin da ake ci gaba da bayyana ta’aziyya da addu’o’i.

Mutane da dama sun bayyana alhininsu kan rasuwar Sarkin, tare da addu’ar Allah Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya jiƙansa da rahama, Ya kuma yafe masa.

Ana roƙon Allah Ya sanya Aljannar Firdausi ta kasance makomar marigayin, Ya haskaka kabarinsa, Ya kuma sa ayyukansa na alheri su zama sanadin samun rahama.

Haka kuma, ana addu’ar Allah Ya bai wa iyalan marigayin, ‘yan uwansa, abokansa da al’ummar Bolari ƙarfin gwiwa da haƙurin jure wannan babban rashi.

Majiyar ta ce:

"Allah Ya yi wa Sarkin Bolari, Alhaji Ahmad Abubakar, rasuwa cikin daren nan, marigayin ya rasu ne bayan wani yanayi na rashin lafiya, kamar yadda bayanan da aka samu suka tabbatar.
Rasuwarsa ta jefa al’ummar Bolari da sauran jama’ar Jihar Gombe cikin alhini da jimami, inda ake ta bayyana alhini da addu’o’i ga marigayin."

Kara karanta wannan

An tafka babban rashi: Tsohon sakataren gwamnati ya riga mu gidan gaskiya

An yi rashin Hakimin Bolari a Gombe
Taswirar jihar Gombe da aka yi rashin Hakimin Bolari. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda mutuwar basaraken ya jawo jimami

Rasuwar Sarkin ta kasance babban rashi ga al’ummar Bolari, musamman duba da irin matsayinsa da muhimmancin da yake da shi a tsakanin jama’ar yankin.

Al’umma na ci gaba da tura sakonnin ta’aziyya ga iyalan marigayin, tare da roƙon Allah Ya ba su ikon jure wannan lokaci mai cike da jimami.

Ana kuma kira ga jama’a da su ci gaba da yi wa marigayin addu’a, domin Allah Ya gafarta masa, Ya jiƙansa, Ya kuma saka shi Aljannar Firdausi.

Wani dan uwan marigayin, Hassan Saleh ya bayyana kaduwarsa game da rashin da aka inda ya yi masa addu'o'in samun rahama.

Saleh ya bayyana a Facebook cewa za a gudanar da Sallar Jana’izarsa da misalin ƙarfe 2:30 na rana a Fadar Hakimin Bolari.

Shugaban NPC, Aminu Wushishi ya rasu

Mun ji cewa Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa, NPC ya rasu ranar Juma’a, 28 ga Agusta 2026, bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kebbi ya kafa sashen kula da kiristoci, an ji dalili

Labarin rasuwarsa ya isa Minna, babban birnin Niger, lokacin sallar Juma’a, lamarin da ya jefa ‘yan siyasa da abokan huldarsa cikin jimami.

Mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Stanley Nwosu, ya tabbatar da rasuwar, yana mai cewa Wushishi ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.