Gwamna Dauda Ya Kadu kan Rasuwar Babban Sarki Mai Daraja a Zamfara

Gwamna Dauda Ya Kadu kan Rasuwar Babban Sarki Mai Daraja a Zamfara

  • Sarkin Zamfaran Zurmi, Alhaji Bello Sulaiman, ya rasu a ranar Litinin, 31 ga watan Agustan 2026 a asibitin Federal Medical Centre da ke Gusau bayan fama da rashin lafiya
  • Gwamna Dauda Lawal ya bayyana rasuwar sarkin a matsayin babban rashi ga iyalansa, masarautar Zurmi da al’ummar jihar Zamfara
  • Dauda Lawal ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa marigayin, ya ba shi Aljannar Firdausi tare da ba iyalansa ƙarfin jure rashin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Gusau, Zamfara - Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana matuƙar alhini bisa rasuwar Sarkin Zamfaran Zurmi, Mai Martaba Alhaji Bello Sulaiman.

Sarkin ya rasu ne a ranar Litinin, 31 ga watan Agustan 2026 a asibitin Federal Medical Centre da ke Gusau, lamarin da ya jefa masarautar Zurmi da al’ummar jihar cikin jimami.

Kara karanta wannan

Babbar nasara: Sojoji sun kashe manyan kwamandojin ’yan ta’adda 2 a Katsina

Gwamna Dauda ya yi ta'aziyya
Gwamna Dauda Lawal na Zamfara da marigayi sarkin Zurmin Zamfara Hoto: Sulaiman Bala Idris
Source: Facebook

Gwamna Lawal ya yi ta'aziyyar babban rashin

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris, ya sanya wa hannu kuma ya fitar a shafinsa na Facebook, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana rasuwar sarkin a matsayin babban rashi.

Gwamnan ya ce mutuwar sarkin ba ta shafi iyalansa kaɗai ba, domin ta kasance babban rashi ga Masarautar Zurmi, cibiyar sarauta ta gargajiya da kuma daukacin al’ummar Jihar Zamfara.

Dauda Lawal ya ce Alhaji Bello Sulaiman zai kasance abin tunawa saboda irin hidimar da ya yi wa jama’arsa da kuma gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban masarautar gargajiyar.

‘Ya sadaukar da kansa wajen zaman lafiya’

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana marigayin a matsayin wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen hidimtawa al’ummarsa tare da nuna kishin zaman lafiya da ci gaban Jihar Zamfara.

Ya ce rasuwar sarkin ta bar babban gibi, musamman saboda irin gudunmawar da ya bayar wajen tafiyar da harkokin masarautar da jin daɗin al’ummar yankin.

Kara karanta wannan

Zulum ya kori dagatai da masu unguwanni a Borno saboda wani dalili

Dauda Lawal ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, Majalisar Masarautar Zurmi da daukacin al’ummar da ke yankin Masarautar Zurmi.

Gwamna ya yi addu’ar samun Aljanna

Gwamna Dauda Lawal ya roƙi Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta wa Alhaji Bello Sulaiman kura-kuransa, Ya saka masa da ayyukan alheri da ya aikata.

Ya kuma roƙi Allah ya sanya shi cikin Aljannar Firdausi tare da ba iyalansa da al’ummar Zurmi ƙarfin jure wannan babban rashi.

Gwamnan ya ce gwamnatin Jihar Zamfara da al’ummar jihar suna tare da iyalan marigayin a wannan lokaci na jimami.

Gwamna Dauda Lawal ya yi ta'aziyya
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Tsohon shugaban AFAN ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kungiyar manoma ta Najeriya (AFAN) da kungiyar masu kiwon kaji ta Najeriya (PAN), Ibrahim Kabir Faskari ya rasu a Turkiyya.

Ibrahim Kabir Faskari, wanda kuma shi ne shugaban Agriculture Business Group, ya rasu a birnin Istanbul bayan fama da matsalolin lafiya da suka biyo bayan tiyatar prostate.

A tsawon rayuwarsa, ya yi fice wajen magana kan matsalolin da ke addabar manoma da masu kiwon kaji, da kuma hanyoyin bunƙasa samar da abinci a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng