"Zan Fadi Abin da Zai Iya Girgiza Kasar"; Omokri Ya Fayyace Bayanan Tinubu da Ke Hannun FBI

"Zan Fadi Abin da Zai Iya Girgiza Kasar"; Omokri Ya Fayyace Bayanan Tinubu da Ke Hannun FBI

  • Reno Omokri ya yi maganan kan bayanan da hukumar FBI take da su kan shugaban kasa Bola Tinubu
  • Tsohon hadimin shugaban kasar ya ce akwai bambanci tsakanin bayanan da FBI ke adanawa da kuma bayanan laifuka na mutum.
  • Omokri ya ce bayanan FBI na iya ƙunsar bayanan mutum da suka shafi biza, bayanan halitta da sauran bayanai na sirri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jakadan da aka naɗa zuwa Mexico, Reno Omokri, ya yi sabon bayani kan bayanan da hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka (FBI) take da su kan Shugaba Bola Tinubu.

Reno Omokri ya yi ikirarin cewa bayanan Shugaba Tinubu da hukumar FBI ke da su ba su nuna cewa ya aikata wani laifi ba.

Omokri ya yi magana kan Tinubu
Reno Omokri na gaisawa tare da Shugaba Bola Tinubu Hoto: Reno Omokri
Source: Twitter

Jaridar TheCable ta ce Omokri ya bayyana hakan ne yayin wani shirin tattaunawa na City Boy Movement (CBM), inda Otega Ogra, hadimi ga Shugaba Tinubu da wasu ‘yan jarida suka halarta.

Kara karanta wannan

Atiku ya ɗauki alkawarin da zai faranta wa ɗaliban Najeriya rai kan kuɗin NELFUND

Omokri ya bambanta tsakanin bayanan FBI da tarihin laifi

Tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasar ya ce akwai babban bambanci tsakanin “FBI records” wato bayanan da FBI ke da su, da kuma “FBI criminal records” wato bayanan da ke nuna tarihin aikata laifi.

A cewarsa, kasancewar FBI na da bayanan mutum ba lallai ne hakan yana nufin an taɓa zarginsa ko samun sa da aikata laifi ba.

Omokri ya yi ikirarin cewa mutanen da suka nemi takardar bizar Amurka na iya samun bayanansu a tsarin FBI saboda binciken bayanan da hukumomin Amurka ke gudanarwa.

‘Babu tarihin laifi na Tinubu a FBI’

Omokri ya ce babu wani bayanan FBI da ke nuna cewa Shugaba Tinubu yana da tarihin aikata laifi.

“Babu wani tarihin laifi na Shugaba Bola Tinubu a FBI. Babu irin wannan abu,” in ji Omokri.

Ya ƙara da cewa ‘yan takarar shugaban ƙasa ma na iya kasancewa da bayanai a hannun FBI saboda mu’amalarsu da hukumomin Amurka.

Kara karanta wannan

Lauya ya tsage gaskiya, an ji dalilin da ya sa Amurka ba ta kama Shugaba Tinubu ba

“Zan fadi abin da zai iya girgiza kasar nan. Dukkan ‘yan takarar wannan zaɓen suna da bayanan FBI. Bayani dai bayani ne. Akwai bambanci tsakanin bayanai da bayanan laifi,” in ji shi.

Ya ce bayanan na iya ƙunsar bayanan sirri

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa Tinubu ba ya son a wallafa bayanan da FBI ke da su, Omokri ya ce irin waɗannan bayanai na iya ƙunsar muhimman bayanan sirri na mutum.

Ya lissafa bayanan halitta, kamar hoton yatsu da na idanu, da sauran bayanan da ake iya samu yayin binciken mutum.

A cewarsa, wasu bayanai na iya shafar iyali da sauran abubuwan sirri, don haka ba kowane mutum ne zai so a bayyana su ga jama’a ba.

Omokri ya kalubalanci masu neman a fitar da bayanan

Omokri ya ce mutanen da ke neman a bayyana bayanan Tinubu na FBI ya kamata su kasance a shirye su amince da irin wannan mataki idan ya shafe su da kansu.

Ya ce bai kamata a yi amfani da batun bayanan FBI wajen nuna cewa mutum yana da hannu cikin aikata laifi ba tare da wata hujja ba.

Kara karanta wannan

Omokri ya fitar da takardar da Amurka ta yi bayani game da Tinubu

Reno Omokri ya yi maganganu kan Tinubu
Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri Hoto: Reno Omokri
Source: Getty Images

Batun bayanan FBI ya shiga kotu

Kalaman Omokri sun zo ne yayin da ake ci gaba da samun ce-ce-ku-ce kan wani shari’a a Amurka da ta shafi buƙatar samun bayanan binciken FBI da suka shafi Tinubu daga shekarar 1992 zuwa 1993.

Batun ya janyo muhawara a Najeriya, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

APM ta bukaci Tinubu ya fasa takara a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar APM ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya sake tunanin neman wa’adi na biyu a zaben shekarar 2027.

Jam'iyyar APM ta bayyana cewa akwai wasu tambayoyi da ba a warware ba kan zargin alaƙarsa da wani binciken miyagun ƙwayoyi a Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng