'Ya Fi Mana Buhari': Kiristocin Arewa Sun Fadi yadda Aka Ci Moriyar Mulkin Tinubu
- Kungiyar Kiristocin Arewa sun bayyana ayyukan alherin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu musamman a yankinsu
- Kiristocin sun bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta fi ta Muhammadu Buhari aiki, kuma Arewa na cin gajiyar ayyukanta
- Kungiyar ta bayyana manyan ayyukan tituna a Arewa, ciki har da Akwanga-Maiduguri, Jos-Jalingo da Sokoto-Lagos, yana mai cewa sun rage wahalhalun sufuri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja — Shugaban kungiyar Kiristocin Arewa, NCA, Rabaran John Hayab, ya yi magana kan ayyukan gwamnatin Bola Tinubu.
Hayab ya ce ya kamata a yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan ayyukan raya kasa da ake gudanarwa a yankin Arewa.

Source: Twitter
Da yake magana da Vanguard, shugaban NCA ya ce bai kamata amincewa da nasarorin gwamnati ya hana mutanen Arewa neman karin ayyuka daga gwamnatin tarayya ba.
Amfanin gwamnatin Tinubu ga Arewa
Ya ce ba zai yiwu Arewa ta yi ikirarin cewa ba ta amfana da gwamnatin Tinubu ba, musamman idan aka yi la’akari da manyan ayyukan more rayuwa da ake gudanarwa.
Sai dai Hayab ya ce wadannan ayyukan ba su magance wasu daga cikin manyan matsalolin Arewa ba, musamman rashin tsaro, yunwa da talauci.
Ya yi nuni da manyan ayyukan tituna da ake gudanarwa a yankin, ciki har da hanyoyin Akwanga zuwa Maiduguri, Jos zuwa Jalingo, Kaduna-Birnin Gwari-Mokwa-Lagos da Sokoto-Lagos.
Ya ce:
“Dubi hanyoyin da suka tashi daga Akwanga da za su kai har Maiduguri. Dubi hanyoyin da suka tashi daga Jos da za su kai Jalingo. Wadannan hanyoyi ne masu matukar muhimmanci.”
Hayab ya kwatanta ayyukan gwamnatin Tinubu da yadda tsohuwar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta gudanar da ayyukanta, musamman kan hanyar Kaduna-Abuja.
Ya ce hanyar Kaduna-Abuja ta shafe shekaru ana alkawarin kammala ta, amma ba a kammala aikin ba a lokacin mulkin Buhari.
Ya ce:
"Buhari bai yi abin da ya kamata ba, kuma su sun fi shi kokari. To, me ya sa ba za ku amince da hakan ba? Domin ba a yi wadannan ayyukan kyauta ba. An kashe makudan kudade wajen gudanar da su.
"A gaskiya, duk shekarun da Buhari ya yi yana mulki, ya kamata a kammala hanyar Kaduna. Amma suna ta wasa da lamarin. Mutane suna rasa rayukansu; ba su damu ba. Akalla wadannan suna kokari.”

Source: UGC
Ayyukan da Tinubu ke yi a Arewa
Shugaban NCA ya ce ana kuma ganin ci gaba a hanyar Abuja zuwa Makurdi, inda ingantuwar yanayin hanya ta rage lokacin tafiya sosai.
Ya kara da cewa kammala gadar sama ta Mararaba zai kara rage wahalhalun da masu amfani da hanyar ke fuskanta.
Baya ga ayyukan more rayuwa, Hayab ya ce Arewa ta samu muhimmiyar wakilci a gwamnatin Tinubu, ciki har da shugabancin jam’iyyar APC da muhimman mukaman ministoci.
Ya ce:
“Arewa tana nan. Dan Arewa ne shugaban jam’iyyar sa. Dan Arewa ne Ministan Yada Labarai. Dan Arewa ne Ministan Tsaro. Ministocin Tsaro guda biyu duk ‘yan Arewa ne.”
Hayab ya ce irin wannan ci gaba ya shafi Kudancin Kaduna, inda ya ambaci kafa Jami’ar Tarayya da Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya a matsayin wasu bukatun da aka dade ana nema.
An shawarci Tinubu ya hakura da takara
An ji cewa jam'iyyar APM ta buƙaci Bola Tinubu ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2027 har sai an warware tambayoyin da suka shafi zargin alaƙarsa da miyagun ƙwayoyi
Jam’iyyar ta yi nuni da shigar da kara da aka yi a kotun Amurka da ke Washington, D.C., kan neman a saki wasu bayanai da ake zargin suna da alaƙa da shugaba Tinubu.
A bayanan da APM ta yi, ta ce Najeriya na buƙatar shugaban ƙasa wanda tarihinsa ba shi da wasu tambayoyi da ba a warware ba kan gaskiya da amana a tarihinsa.
Asali: Legit.ng


