Garabasa ga Ƴan Najeriya, Gwamnatin Tinubu Za Ta Samar da Ayyuka Miliyan 1
- Gwamnatin Tarayya ta sanya burin samar da ayyukan yi ga ’yan Najeriya da za a danganta da fitar da ayyuka zuwa ketare
- An ƙaddamar da shirin domin haɗa ƙwararrun ’yan Najeriya da kamfanoni da ma’aikata na ƙasashen duniya, ba tare da ƙaura daga Najeriya ba
- Gwamnati ta ce sama da ’yan Najeriya 200,000 na samun horo a cibiyoyin ƙwarewa 1,200, yayin da ake shirin kafa makarantar fasahar zamani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta sanya burin samar da ayyukan yi miliyan ɗaya da ke da alaƙa da fitar da ayyuka zuwa ƙasashen waje.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa ana sa ran hakan nan da 2030, yayin da take ƙoƙarin mayar da ƙwararrun ’yan Najeriya da ayyukan da ake gudanarwa ta hanyar fasaha.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da ma'aikatar yada labarai da wayar da kan al'umma ta wallafa a shafinta na Facebook.
Gwamnatin ta ƙaddamar da shirin “Hire from Nigeria” a Abuja, inda Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dr Jumoke Oduwole ta tabbatar a wani taro, cewar Punch.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris; da Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, suka bayyana matakan haɗa ƙwararrun ’yan Najeriya da masu ɗaukar ma’aikata da ’yan kasuwa a kasuwannin duniya.
Oduwole ta ce shirin wani tsari ne na tattalin arziki da aka tsara da gangan, ba wani kamfen na talla kawai ba, inda ta jaddada cewa Najeriya za ta iya amfani da yawan jama’arta da ƙwararrun ma’aikatanta wajen faɗaɗa fitar da ayyuka zuwa ƙasashen waje.
Ta ce Gwamnatin Tarayya na samar da dabarun fitar da ayyuka zuwa ƙasashen waje bisa buƙatun kasuwa, da kuma manufar farko ta ƙasa kan harkokin outsourcing, wadda ake sa ran ƙaddamar da ita a watan Nuwamba 2026.

Source: Facebook
Minista ya fadi muhimmancin shirin a Najeriya
Idris ya ce shirin zai bai wa ’yan Najeriya damar samun kuɗi daga kasuwannin duniya ba tare da barin ƙasar zuwa ƙasashen waje ba, musamman saboda fasahar dijital na ba da damar gudanar da ayyukan ƙwararru tsakanin ƙasashe.
A cewarsa, za a yi amfani da hanyoyin sadarwa da hukumomin gwamnati wajen tallata ƙwarewar ’yan Najeriya a duniya, ciki har da gabatar da shirin a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 da aka shirya.
Alausa ya ce ana daidaita ɓangaren ilimi da shirin domin samar da ƙwararrun ma’aikata da suka shirya shiga masana’antu kuma za su iya yin gogayya a duniya.
Ya bayyana cewa a halin yanzu sama da ’yan Najeriya 200,000 na samun horo a cibiyoyin koyar da ƙwarewa sama da 1,200, yayin da ake shirin kafa Digital Technology Academy da za ta mayar da hankali kan basirar wucin gadi.
An bude shafin daukar matasa aiki
Mun ba ku labarin cewa kungiyar ECOWAS ta buɗe shafin neman guraben shiga shirin horas da matasa na shekara guda ga ƴan Najeriya da sauran ƙasashen yammacin Afirka.
Shirin zai bai wa waɗanda aka zaɓa damar yin aiki tare da hukumomin ECOWAS cikin cikakken tallafin kuɗi tare da samun horo da jagoranci.
Masu sha'awar shiga shirin dole su kasance 'yan ƙasa membobin ECOWAS, ba su wuce shekara 32 ba, kuma su mallaki digiri daga jami'a.
Asali: Legit.ng


