
Ayyuka mafi kyawu a Najeriya







Hukumar EFCC ta ce duk wanda ya taka doka za ta taka shi, ta sanar da korar jami'anta 27 daga aiki bayan samunsu da laifin cin hanci da rashin ɗa'a.

Gwamna Monday Okpebholo na Edo ya sallami dukkan ƴan majalisar gudanarwa na manyan makarantun gaba da sakandire mallakin gwamnatin jihar Edo nan take.

Majalisar wakilan kasar nan ta bijiro da kudirin da zai rika sa wa shugaban kasa linzami kan gudanar da gwamnati tare da tabbatar da ba da bayanan ayyuka.

Gwamnatin Kano ta bayyana shirinta na ɗaukar jami'an tsaro musamman mafarauta aikin gadin makarantu gwamnati a faɗin kananam hukumomi 44 a jihar.

Ana hasashen 'Hamster' na shirin fashewa, asibitin Gwamnatin Tarayya (FTH) da ke Gombe ya haramtawa ma'aikata 'kirifto' da 'mining' yayin da suke bakin aiki.

Gwamnan jihar Ekiti Biodun Oyebanji ya amince da tsarin aiki daga gida domin saukakawa ma'aikata sakamakon tsadar rayuwar da aka shiga saboda tashin fetur.

Gwamna Nasir Idris Ƙauran Gwandu ya ce gwamnatinsa a shirye take ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000, ya yiwa ma'aikaya alƙawari.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta samar da ayyukan yi ga matasan kasar nan fiye da miliyan 2 a ɓangaren nishaɗi da fasaha ta ma'aikatar fasaha da al'adu.

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf a Kano ta amince da fitar da N268,160,455.84 domin samar da wasu manyan ayyukan a fadin jihar domin amfanar da jama'a.
Ayyuka mafi kyawu a Najeriya
Samu kari