Maulidin Annabi SAW: Sakon Gwamna Abba Kabir ga Al’ummar Musulmi
- Gwamnan Kano, Abba Yusuf, ya shawarci al'ummar Musulmi su sabunta riko da koyarwar Annabi Muhammad
- Abba Kabir ya bayyana Takutaha a matsayin al’ada mai muhimmanci ta addini da al’adu, wacce ke hada kan al’ummar Kano
- Gwamnan ya bukaci matasa su taka muhimmiyar rawa wajen kare tarihin Kano da al’adunta, tare da tabbatar da zaman lafiya da hadin kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Gwamnan Kano, Abba Yusuf, ya shawarci al'ummar Musulmi yayin bikin Maulidin Annabi SAW.
Gwamnan ya shawarci Musulmi a fadin Kano su yi amfani da bikin Takutaha Maulud wajen sabunta alkawarinsu na bin koyarwar Annabi Muhammad (SAW).

Source: Facebook
Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Dawakin-Tofa, ya fitar a Facebook yayin da Musulmi ke bikin Takutaha na tunawa da haihuwar Annabi mai daraja.
Bukatar Abba Kabir ga al'ummar Musulmi
Ya ce musamman ya kamata su mai da hankali kan zaman lafiya, tausayi, adalci, hakuri da fahimtar juna, wadanda ke daga cikin muhimman darussan rayuwar Annabi.
Gwamnan ya bayyana Takutaha a matsayin muhimmiyar al’ada ta addini da al’adu, wadda ta dade tana hada kan mazauna Kano tare da ba su damar yin tunani kan rayuwa da koyarwar Annabi.
Ya bukaci Musulmi su tabbatar da cewa dabi’un da ake koyarwa a lokacin bikin sun kasance wani bangare na rayuwarsu ta yau da kullum, musamman yadda suke mu’amala da juna.
Gwamnan ya kuma bukaci kara himma wajen tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna, yana mai cewa wadannan dabi’u suna da muhimmanci wajen tabbatar da kwanciyar hankali da ci gaban jihar Kano.

Source: Twitter
Shawawar Abba Kabir ga mazauna Kano
Haka kuma, Abba Kabir ya bukaci mazauna Kano su ci gaba da nuna hadin kai da ‘yan uwantaka da aka gani yayin bikin, yana mai cewa bukukuwan addini ya kamata su karfafa alaka tsakanin al’ummomi.
Ya yaba wa sarakunan gargajiya, malaman addini, shugabannin al’umma da masu shirya Takutaha saboda kokarinsu na kare tarihin addini da al’adun Kano.
Gwamnan ya tabbatar wa mazauna Kano cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen da ke inganta tarihi, al’adu da dabi’un addini na Kano.
Ya kuma bukaci matasa su taka muhimmiyar rawa wajen kare tarihin addini da al’adun Kano, domin su tabbatar da ci gaba da wanzuwar abubuwan tarihi.
Abba Kabir ya yi wa al’ummar Kano fatan samun bikin Takutaha mai cike da zaman lafiya da nasara, tare da addu’ar samun ci gaba da kwanciyar hankali da wadata a Kano.
An kashe matashi a hanyar dawowa daga Maulidi
An ji cewa an tabbatar da cewa daba sun kashe wani matashi mai suna Yusuf Ahmad a unguwar Dorayi da ke karamar hukumar Gwale a Kano.
Bayanan da ke fitowa sun nuna cewa lamarin ya biyo bayan rikicin ramuwar gayya da ya samo asali daga jikkata wani matashi a unguwar.
Dakarun yan sanda sun ce an kama wasu da ake zargi da hannu a kashe Yusuf, wanda ya dawo daga wurin Maulidi yayin da bincike ke ci gaba.
Asali: Legit.ng

