Duk wanda bai nuna shaidar ya yi NYSC ba kada a dauke shi aiki, DG ya ja kunne

Duk wanda bai nuna shaidar ya yi NYSC ba kada a dauke shi aiki, DG ya ja kunne

  • Darakta-janar na hukumar NYSC ya ce kada a dauki duk wanda bai nuna takardar shaidar kammala NYSC aiki
  • Ya shawarci masu daukar ma'aikata da su turo ma'aikatansu dake aiki a yanzu don gudanar da bincike akansu
  • A baya an yi cece-kuce kan batun dakatar da shirin NYSC kwata-kwata a Najeriya saboda wasu dalilai

Darakta-Janar na hukumar bautar kasa ta kasa (NYSC), Birgediya-Janar Shuaibu Ibrahim, ya bukaci masu daukar ma’aikata da kada su dauki tsofaffin ‘yan yi wa kasa hidiman da ba su gabatar da sahihan takardun NYSC ko takardar izinin dage shirin akansu ba.

Ya yi magana ne a Abuja a jiya yayin taron karawa juna sani na shari'a mai taken "Nazarin dokokin da ke tsara yadda ake amfani da fasahar sadarwa ta zamani a Najeriya tare da Nuni Musamman kan Ka'idojin Kare Bayanai"

Ya yi misali da tanadin dokar NYSC wacce ta ce saboda manufar daukar aiki a ko’ina a Najeriya, kowane mai daukar aiki yana bukatar neman takardar shaidar kammala karatu ciki har da na bautar kasa, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Duk da tsawon tarihin Gurasa a Kano, 'yan Gurasa sun yi barazanar daina sana'ar

Duk wanda bai yi NYSC ba kada a dauke shi aiki, DG na NYSC ya ja kunne
Mambobin bautar kasa ta NYSC | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya shawarci masu daukar ma’aikata da su gabatar da takardun NYSC na ma’aikatan da suke da su a cikin shirin don tabbatarwa idan akwai bukatar hakan.

Ya ce bitar za ta yi amfani da damar da lauyoyi 'yan bautar kasa ke da shi don inganta ayyukan shari'a ga al'umma da kuma daidaita ayyukan shirin ba da taimakon shari'a na kasa baki daya.

Dan majalisar wakilai ya yi kira da a soke shirin bautar kasa na NYSC

Awaji Inombek Abiante, dan majalisar wakilai a kwanakin baya ya dauki nauyin wani kudiri da ke ba da shawarar a soke Hukumar bautar kasa (NYSC), The Guardian ta ruwaito.

Kudurin nasa ya jawo cece-kuce cikin al'umma, yayin da wasu fitattun 'yan Najeriya ke tofa albarkacin bakinsu game dashi.

Tun farko an kafa tsari na NYSC ne don dinke baraka tsakanin kabilu da addinai a cikin kasar da kuma karfafa ruhin kishin kasa, wanda wasu suke ganin soke shi zai haifar da wasu sabbin matsaloli.

KU KARANTA: Majalisa za ta binciki gwamnatin Buhari kan shirin farfado da tattalin arziki

Wasu jami'o'in Kotono 8 da dalibansu ba a amince su yi bautar kasa ba (NYSC)

A wani labarin, Hukumar Kula da Matasa ta Kasa (NYSC), ta hana daliban da suka kammala karatu a jami’o’in kasashen waje guda takwas da ke Jamhuriyar Benin, Nijar da Kamaru daga shiga shirin bautar kasa na shekarar 2021.

An tattaro cewa jami'o'in, wadanda galibinsu suna bayar da digiri ne 'yan watanni kadan bayan shiga makarantun, ana kuma kiransu da "Jami'o'i Cotono".

A wata madauwari ta haramcin, mai dauke da kwanan wata 5 ga Maris, 2021, wanda aka jingina ga Kodinetan Jiha/Babban Birnin Tarayya kuma Daily Nigerian ta gani, ba a bayyana dalilin cire jami'o'in ba a hukumance.

Asali: Legit.ng

Online view pixel