An Yi Rashi: Shugaban Hukumar Kidaya Ta Ƙasa, NPC Ya Yi Bankwana da Duniya
- Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa, NPC ya rasu ranar Juma’a, 28 ga Agusta 2026, bayan fama da gajeriyar rashin lafiya
- Labarin rasuwarsa ya isa Minna, babban birnin Niger, lokacin sallar Juma’a, lamarin da ya jefa ‘yan siyasa da abokan huldarsa cikin jimami
- Mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Stanley Nwosu, ya tabbatar da rasuwar, yana mai cewa Wushishi ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Minna, Niger - Rahotanni sun bayyana cewa shugaban hukumar kidaya ta kasa, NPC ya riga mu gidan gaskiya.
Dakta Aminu Wushishi ya rasu ranar Juma’a, 28 ga Agusta 2026, bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Source: Original
Mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Stanley Nwosu, ya tabbatar Vanguard labarin rasuwar shugaban NPC.
An yi rashin shugaban hukumar kidaya

Kara karanta wannan
Harald V: Babban sarkin da ya fi tsufa a Turai ya rasu bayan shekara 35 a karagar mulki
Labarin rasuwarsa ya isa Minna, babban birnin Niger, a daidai lokacin sallar Juma’a, lamarin da ya jefa abokansa da ‘yan siyasa cikin jimami.
Wushishi, wanda ya taba zama Sakataren jam’iyyar PDP, mai adawa reshen Niger, an ce ya yi fama da rashin lafiya na wani dan lokaci kafin rasuwarsa.
Ya ce:
“Eh, gaskiya ne. Shugaban NPC ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya."
Ya zuwa lokacin da aka hada wannan rahoto, har yanzu ana jiran karin bayani kan musabbabin rasuwarsa da kuma shirye-shiryen jana’izarsa.
Wata majiya daga hukumar ta shaida wa Daily Trust cewa Yusuf ya rasu a Asibitin Nizamiya da ke Abuja bayan ya dawo daga sallar Juma’a.
Majiyar ta ƙara da cewa ya fara rashin lafiya ne kwanaki biyar da suka gabata, lokacin da yake shirin tafiya Rwanda.
A cewar majiyar, shugaban NPC ɗin yana fama da matsalolin lafiya da aka bayyana cewa suna da alaƙa da ciwon sukari kafin rasuwarsa.
An ce Yusuf ya kuma taɓa suma ko faɗuwa a lokuta da dama a ofishinsa da kuma yayin wasu tarukan jama’a.

Source: Facebook
Yaushe Wushishi ya zama shugaban NPC
An naɗa Yusuf a matsayin shugaban Hukumar Ƙidayar Jama’a ta Ƙasa (NPC) ne daga Shugaba Bola Tinubu a shekarar 2025, daga bisani kuma Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin nasa.
Shugaba Tinubu ne ya rantsar da shi a ranar 3 ga Disamba, 2025, tare da wasu mambobi biyu na hukumar NPC.
Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana shi a matsayin shugaban hukumar mai shekaru 65 a lokacin rantsar da shi.
Ta kuma tabbatar da cewa Yusuf ya fara gudanar da ayyukansa a hukumance a matsayin shugaban hukumar bayan an rantsar da shi a Abuja a ranar 3 ga Disamba, 2025.
Tsohon mataimakin ggwamnan Bauchi ya rasu
A baya, an ji cewa mun samu labarin rasuwar tsohon gwamnan jihar Bauchi kuma wazirin Katagum, Arch. Audu Sule Katagum a safiyar yau Asabar, 20 ga Yuni, 2026.
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin, tare da addu'ar Allah Ya masa rahama.
Ya bayyana marigayi Wazirin Katagum a matsayin shugaba kuma tsayayyen dattijo, wanda rashinsa babban gibi ne ga jihar Bauchi.
Asali: Legit.ng
