'Jami'an tsaro na IPOB sun halaka Hausawa 4 a Imo'

'Jami'an tsaro na IPOB sun halaka Hausawa 4 a Imo'

- Jami'an tsaro na kungiyar IPOB masu fafutikar kafa Biafra sun kashe hausawa hudu a jihar Imo a cewar hausawan

- Wani mazaunin unguwar Olru, Yusuf, inda ya abin ya faru ya ce tuni an yi musu jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada

- Yusuf ya ce lamarin ya faru ne a yayin da mutanen unguwar suka ki amincewa su biya wata haraji da yan kungiyar ta IPOB suka kakaba musu

Hausawa mazauna unguwar Orlu a jihar Imo, sun yi zargin cewa jami'an hukumar tsaro da kudancin Nigeria da haramtaciyar kungiyar fafutikan kafa kasar Biafra, IPOB, ta ka kafa sun kashe hausawa hudu a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutane da dama kana an lalata kadarori yayin da 'yan kungiyar tsaron na IPOB suka yi arangama da yan sanda da sojoji a Orlu.

'Jami'an tsaro na IPOB sun halaka Hausawa 4 a Imo'
'Jami'an tsaro na IPOB sun halaka Hausawa 4 a Imo'. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kada su sake ku kusanci dazukan mu, 'Yan kabilar Ijaw sun gargadi makiyaya

Wani mazaunin unguwar wanda ya ce sunansa Yusuf saboda dalilin tsaro ya ce dakarun sojojin Najeriya ne suka kawo musu dauki yayin da aka kai musu harin.

Ya ce sojojin sun mika gawarwakin wadanda suka rasu ga shugabannin Hausawa a garin kuma tuni an musu jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci.

"An kwaso gawarwarkin wadanda suka rasu daga wuraren da suke kasuwancinsu," in ji shi.

Da ya ke bada bayani kan yadda abin ya faru, Yusuf ya ce: "Abin ya fara ne a ranar Alhamis a lokacin da mutanen gari suka ki biyan harajin da IPOB ta dora musu. Saboda fusata su da abin ya yi, sun tafi su kona fadar sarkin Orlu (Orlu Eze)."

KU KARANTA: Sojoji sun sada ƴan Boko Haram 8 da mahallacinsu bayan musayar wuta a Borno da Yobe

Yusuf ya kara da cewa a lokacin zanga zangar Endsars, an halaka Hausawa fiye da 40 a Imo, inda ya ce kafafen watsa labarai ba su wallafa rahoton ba kuma ba a dauki wani mataki a kai ba.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel