Jami'an Tsaro Sun Kutsa cikin Daji, Sun Kubutar da Matasan NYSC da Aka Yi Garkuwa da Su

Jami'an Tsaro Sun Kutsa cikin Daji, Sun Kubutar da Matasan NYSC da Aka Yi Garkuwa da Su

  • Jami’an tsaro sun kubutar da matasan NYSC 10 daga cikin 15 da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace a jihar Kogi
  • An kubutar da wadanda aka sace ne a dajin Egume da ke karamar hukumar Ofu kwanaki kadan bayan an yi garkuwa da su
  • Jami’an tsaro na ci gaba da aikin ceto sauran wadanda aka sace da kuma cafke masu garkuwa da mutanen domin doka ta yi aiki a kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kogi, Nigeria - Jami’an tsaro sun kubutar da matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC) 10 daga cikin 15 da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace a jihar Kogi ranar Juma’a da ta wuce.

Daraktan Ayyukan Yada Labarai na Tsaro, Manjo-Janar Michael Onoja, ne ya bayyana hakan, inda ya ce an kubutar da su ne ranar Litinin a dajin Egume da ke karamar hukumar Ofu.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta hango matsala, Ribadu ya yi gargadi kan barazanar tsaro a wasu wurare

Sojoji.
Dakarun sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: Nigerian Army
Source: Facebook

Jami'an tsaro sun ceto yan NYSC 10

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Onoja ya bayyana haka ne yayin da yake magana a wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar tsaro (DHQ) jiya Litinin 31 ga watan Agusta, 2026.

Manjo Janar Onoja ya ce har yanzu ana ci gaba da aikin kubutar da sauran wadanda aka sace da kuma cafke masu garkuwa da mutanen da suka aikata wannan laifin.

Tun farko dai yan bbindiga sun sace yan bautar kasaa ne ranar Juma’a da ta wuce yayin da suke tafiya daga Abuja zuwa jihar Bayelsa bayan kammala daukar horo s sansanin horas da su.

DHQ ta roki hadin kan jama'a

Onoja ya bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da kasancewa cikin shiri, sannan su gaggauta kai rahoton duk wani abin da suka gani ko bayanin da ka iya taimaka wa jami’an tsaro.

Kara karanta wannan

Ta faru ta ƙare: Sojoji sun shiga maɓoyar ƙasurgumin ɗan bindiga, Kachalla Muhammadu

A cewarsa, hadin kai da bayanan sirri da za a iya samu daga wurin jama'a na iya taimaka wa wajen kubutar da sauran wadanda aka sace da kuma cafke wadanda suka aikata laifin.

Yan NYSC.
Matasa masu yi wa kasa hidima yayin da suke daukar horo a sansanin NYSC Hoto: NYSC
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa masu garkuwa da mutanen sun bukaci iyalan wasu daga cikin wadanda aka sace su biya kudin fansa na Naira miliyan 20 kan kowane mutum daya.

Yan sanda sun ceto mutum 11 a Kogi

A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sanda a jihar Kogi ta samu nasarar ceto mutane 11 da 'yan ta'adda saka yi awon gaba da su, ciki har da 'yan bautar kasa (NYSC) da direbobi guda biyu.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kogi, Saliu Afusat, ta tabbatar da gudanar da aikin ceton a wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma'a da ta gabata.

Afusat ta bayyana cewa jami'an tsaro sun kai dauki cikin hanzari inda suka ceto mutane 11 daga hannun tsagerun, inda ta ce yawancin wadanda aka ceton mambobin NYSC ne da ke kan hanyarsu ta zuwa birnin Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262