Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Sakataren NLC na Kasa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Sakataren NLC na Kasa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Babban sakataren kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Emmanuel Ugboaja ya rasu yana da shekara 60 bayan doguwar rashin lafiya
  • Bayanai sun nuna cewa marigayin ya zama babban sakataren kungiyar NLC na biyar a tarihi a watan Agustan shekarar 2019
  • Emmanuel Ugboaja ya shafe sama da shekaru 30 yana aikin ƙungiyar kwadago ta Najeriya kafin Allah Ya karbi rayuwarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Enugu, Nigeria - Babban Sakatare na kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Kwamared Emmanuel Ugboaja, ya rasu yana da shekara 60 bayan fama da doguwar rashin lafiya.

An bayyana rasuwar Ugboaja ne a ranar Alhamis, 27 ga watan Agustan 2026 a lokacin da Majalisar Zartarwa ta Ƙasa ta NLC ke gudanar da taronta a jihar Enugu.

Emmanuel Ugboaja.
Babban sakataren kungiyar NLC ta Najeriya, Emmanuel Ugboaja Hoto: NLC Nigeria
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa shugaban kungiyar NLC na kasa, Kwamared Joe Ajaero, ne ya sanar da mambobin ƙungiyar labarin rasuwar bayan ya samu wasiƙa daga iyalan marigayin.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya

Tarihin marigayi Emmanuel Ugboaja

Ugboaja, wanda ƙwararren lauya ne kuma gogaggen ɗan ƙungiyar kwadago, ya zama babban sakataren NLC na biyar a watan Agustan 2019, inda ya gaji Peter Ozo-Eson.

Ya yi aiki a ƙungiyar kwadago na tsawon lokacin da ya haura shekaru 30, bayan ya fara aiki a fannin ƙwadago a shekarar 1993, bayan ya shafe kusan shekaru huɗu yana aikin lauya mai zaman kansa.

An haifi marigayi Ugboaja a ranar 15 ga Mayun 1966, kuma ya karanci shari'a a Jami'ar Calabar da ke jihar Cross River, inda ya samu digirinsa a shekarar 1987.

Daga baya ya shiga Ƙungiyar Ma'aikatan Masana'antun Sinadarai, Takalma, Roba, Fata da Kayayyakin da ba na Ƙarfe ba ta Ƙasa, inda ya yi ta samun ƙarin matsayi har ya zama babban sakataren ƙungiyar daga shekarar 2000 zuwa 2005.

Gudunmawarsa ga kungiyar ƙwadago

Bayanan tarihi na NLC sun bayyana Ugboaja a matsayin lauya ɗan Najeriya na farko da ya sadaukar da kansa gaba ɗaya wajen yi wa ƙungiyar kwadago aiki.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya sauka a Kano, ya yi ganawar sirri da Sarki Sanusi II

Baya ga ayyukan ƙungiyar kwadago, ya kuma taka rawa a harkokin ƙungiyoyin fararen hula tare da shiga cikin ayyukan sake fasalin kundin tsarin mulkin Najeriya a shekarun 2005 da 2014.

Kafin a naɗa shi babban sakataren NLC, Ugboaja ya kasance Mataimakin Babban Sakataren Ƙungiyar, inda yake jagorantar sashen hulɗar masana'antu da shirya ayyukan ƙungiyar.

A lokacin da yake shugabantar NLC, ya kasance a sahun gaba wajen wasu manyan shawarwarin ƙungiyar kwadago, ciki har da tattaunawa kan aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi da kuma walwalar ma'aikata.

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262