Kirista Ya Lashe Gasar Kur'ani, Ya Samu Kyautar Kujerar Umrah
- Wani Kirista ɗan ƙasar Masar mai suna Mina ya shiga wata gasa ta addinin Musulunci da ke gwada ilimin Alƙur’ani da wata manufa ta musamman a zuciyarsa
- Mina ya tura amsar da ta dace fiye da sau 50 zuwa 60 domin ƙara damar lashe kyautar tafiyar Umrah kyauta
- Um Ali, maƙwabciyar Musulma da Mina ke fatan taimakawa, ta daɗe tana mafarkin yin Umrah tun tana da ƙarfin tafiya cikin sauƙi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Egypt - Wani Kirista a ƙasar Masar ya yi fice a kafafen sada zumunta bayan ya shiga wata gasa ta addinin Musulunci domin lashe kujerar Umrah kyauta.
Mutumin mai suna Mina, ya ci karo da shirin kai tsaye da mai wa’azin Musulunci Dr Ayman Abu Omar ke gudanarwa, inda ya lura cewa maƙwabciyarsa, wadda aka fi sani da Um Ali ko Mona, tana cikin masu shiga gasar.

Source: Twitter
A cewar Sky News Arabia a X, Mina ya ce a lokacin da ya fahimci irin tsananin burin Um Ali na zuwa Umrah, sai ya yanke shawara cewa zai shiga gasar.
Dabarar lashe kyautar Umrah
Yayin da ya ke bayani game da shiga gasar, matashin ya bayyana cewa:
"Ni Kirista ne, amma na shiga gasar addinin Musulunci,"
Kamar yadda Gulf News ta ruwaito, ya shaida wa Um Ali cewa idan ita ba ta lashe gasar ba, idan ya yi nasara za ta samu damar zuwa Umrah.
Domin neman nasara a gasar, Mina ya tura amsoshi yadda ya kamata tsakanin sau 50 zuwa 60, inda daga ƙarshe aka zaɓe shi a matsayin wanda ya yi nasara.
Um Ali ta ce ta lura cewa shigar Mina cikin gasar na jawo hankali yayin watsa shirye-shiryen kai tsaye, kuma ta bayyana cewa ta cika da farin ciki lokacin da ta gano cewa ya lashe kujerar Umrah.

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya

Source: Facebook
Alakar Mina da Um Ali
Mina ya ce alaƙarsa da Um Ali da iyalanta ta wuce shekaru 20, kuma ta zama wata dangantaka da ta fi ta maƙwabtaka ta yau da kullum karfi.
Ya bayyana Um Ali a matsayin wadda yake ɗauka tamkar babbar yayarsa, inda ya ce yana mu’amala da iyayenta da irin kulawa da girmamawar da yake bai wa iyalansa.
Ga bidiyon bayanin da Mina ya yi a kasa:
Maryam ta lashe gasar Kur'ani
A wani labarin, mun ruwaito cewa Maryam Ibrahim Dan’azumi daga jihar Gombe ta lashe matsayi na farko a rukuni biyu a gasar Alƙur’ani ta ƙasa da ƙasa karo na 46 da aka gudanar a Makka.
Gasar ta samu halartar ’yan takara 334 daga ƙasashe 133, lamarin da ya sa ta kasance gasar da ta samu mafi yawan mahalarta a tarihin taron.
’Yar’uwar Maryam, Hajara, ita ma ta lashe irin wannan gasa ta Alƙur’ani ta ƙasa da ƙasa a ƙasar Jordan a shekarar 2024, lamarin da ya sa ’yan’uwan biyu suka kafa tarihi.
Asali: Legit.ng
