Abin Mamaki: Kirista Ya Gina Masallaci, Gwamnan Nasarawa Ya Yi Hudubar Juma'a
- Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule ya kaddamar da sabon masallacin Juma’a na Dari a karamar hukumar Kokona
- Rahoto ya nuna cewa an gina masallacin ne karkashin kulawar kwamishinan ilimi na jihar, Dr. John D.W. Mamman
- 'Yan siyasa, sarakunan gargajiya da tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu sun halarci bude masallacin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Nasarawa – A jiya Juma’a, 5 ga Satumba, 2025, Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi A. Sule ya kaddamar da sabon masallacin Juma’a na garin Dari.
Taron ya samu halartar jiga-jigan 'yan siyasa, sarakunan gargajiya da al’ummar yankin wadanda suka bayyana farin cikinsu da wannan muhimmin aiki da aka kammala cikin nasara.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka gina masallacin ne a cikin wani sako da aka wallafa a shafin gwamna Sule na dandalin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Sule ya yi hudubar Juma’a
Yayin kaddamarwar, Gwamna Sule ya yi huduba ga jama’a tare da jagorantar raka’o’i biyu na sallar Juma’a a sabon masallacin.
An jaddada cewa ginin masallaci irin wannan na da muhimmanci wajen karfafa hadin kan addini da kyautata rayuwar al’umma.
Sanata Ahmed Wadada Aliyu, wanda ke wakiltar Nasarawa ta Yamma a majalisar dattawa, ya halarci taron tare da sauran manyan baki.
Shi ma ya yi sallar Juma’a a masallacin, yana mai bayyana godiya ga wadanda suka yi aiki tukuru wajen ganin an kammala wannan aiki.
'Yan siyasa da sarakuna sun hallara
Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ma ya halarci kaddamarwar tare da wasu sarakunan gargajiya daga sassan jihar.
Hakan ya nuna irin goyon bayan da wannan aiki ya samu daga manyan shugabanni da masu ruwa da tsaki.
Mahalarta sun yaba da jajircewar Gwamna Sule da kuma irin gudunmawar da Dr Mamman ya bayar wajen tabbatar da cewa al’ummar Dari sun amfana da wurin ibada na zamani.
Wane ne Dr. John D.W. Mamman?
Kwamishinan ilimi a jihar kuma tsohon shugaban APC na Nasarawa, Dr. John D.W. Mamman ne ya jagoranci aikin ginin.
Abin lura shi ne, duk da kasancewarsa Kirista, ya gina wannan masallaci ga musulman yankinsa domin karfafa zaman lafiya da kyakkyawar dangantaka tsakanin addinai.
Shafin Nasarawa Reporters ya wallafa cewa a shekarar 2021 ma, Dr. Mamman ya gina wani masallaci na miliyoyin Naira a garinsa na Dari.

Source: Facebook
A lokacin, ya bayyana cewa manufarsa ita ce ganin an yi rayuwa cikin jituwa tsakanin Kirista, Musulmi da masu bautar gargajiya.
Ya kara da cewa yana tallafa wa mabiyan addinin gargajiya a lokutan bukukuwansu na shekara-shekara.
Daurawa ya yi hudubar Juma'a a Sokoto
A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya jagoranci sallar Juma'a a jihar Sokoto.
Shehin Malamin ya isa jihar Sokoto ne domin halartar taro a jami'ar Usmanu Danfodio da za a ba shi da Dakta.
Rahotanni sun nuna cewa za a karrama Sheikh Daurawa ne tare da wasu mutane yayin da jami'ar ta cika shekara 50 da kafuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

