Harald V: Babban Sarkin da Ya Fi Tsufa a Turai Ya Rasu bayan Shekara 35 a Karagar Mulki
- Sarkin Norway Harald V ya rasu yana da shekaru 89 bayan ya shafe shekaru 35 a kan karagar mulkin ƙasar
- Ɗansa, Haakon, ya gaje shi a matsayin sarki, yayin da jikarsa Ingrid Alexandra ta zama magajiyar sarautar Norway.
- Harald ya yi mulki na tsawon shekaru, inda ya samu karɓuwa saboda sauƙaƙa tsarin masarautar da kusancinsa da al’ummar Norway
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kasar Norway - Sarkin Norway, Harald V, wanda shi ne mafi tsufa cikin sarakunan Turai da ke kan karagar mulki, ya rasu yana da shekaru 89 bayan shafe shekaru 35 yana mulkin ƙasar.
Fadar Masarautar Norway ta sanar da rasuwarsa ranar Juma’a, 28 ga watan Agustan 2026 jim kaɗan bayan ƙarfe 6:35 na safe.

Source: Getty Images
An bayyana cewa ɗansa, Yarima Haakon, ya gaje shi a matsayin sabon sarkin Norway, rahoton tashar CNN ya nuna hakan.
Harald ya rasu ya bar matarsa, Sarauniya Sonja, wadda suka shafe shekaru 57 tare, da ’ya’yansu biyu da jikoki biyar. Jikarsa, Ingrid Alexandra, wadda ita ce ’yar Haakon, yanzu ta zama magajiyar sarautar Norway.
Norway na jimamin rasuwar Sarki Harald
Firaministan Norway, Jonas Gahr Støre, ya bayyana rasuwar Harald a matsayin babban rashi ga ƙasar.
Støre ya ce “ƙasa baki ɗaya tana cikin jimami”, yana mai cewa al’ummar Norway sun rasa wani sarki da ya sadaukar da tsawon rayuwarsa wajen yi wa ƙasar hidima.
Rasuwar sarkin ta zo ne bayan lafiyarsa ta tabarbare a kwanakin baya.
A tsakiyar watan Agusta, an kwantar da Harald a asibiti domin kula da wata matsalar tara ruwa a jiki da aka danganta da wata cuta ta jini.
Daga bisani, ya kamu da cutar bakteriya, lamarin da ya ƙara tsananta yanayin lafiyarsa.
Harald ya gaji mahaifinsa
Harald ya hau karagar mulkin Norway a shekarar 1991, yana da shekaru 53, bayan rasuwar mahaifinsa, Sarki Olav V.
A ranar 23 ga Yuni 1991, Harald da matarsa Sonja sun gudanar da bikin tabbatar da sarautarsu a Cathedral na Nidaros da ke Trondheim.
Bikin ya ƙunshi wasu al’adun masarautar da suka samo asali tun daga zamanin Tsakiyar Turai.
Bayan bikin, ma’auratan sun gudanar da rangadin kwanaki 10 a kudancin Norway, sannan suka sake zagayawa wasu yankunan Arewacin ƙasar a shekarar 1992.
Ya taso a lokacin yaƙi
An haifi Harald a ranar 21 ga Fabrairu 1937, kuma shi ne ƙarami cikin ’ya’ya uku na iyayensa, sannan shi kaɗai ne namiji.
A lokacin, dokar kundin tsarin mulkin Norway ta tanadi cewa maza ne kaɗai za su iya gadon sarauta.
Harald yana da shekaru uku kacal lokacin da sojojin Jamus suka mamaye Norway a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu.
Saboda mamayar, iyalinsa tare da wasu daga cikin gwamnatin Norway suka tsere zuwa Sweden.
Bayan wasu watanni, Harald ya bar Sweden tare da mahaifiyarsa da ’yan uwansa mata zuwa Washington DC da ke Amurka domin samun mafaka.
A wannan lokaci, kakansa, Sarki Haakon VII, da mahaifinsa Olav sun koma London, inda suka ci gaba da kasancewa har zuwa ƙarshen mamayar Jamus.

Kara karanta wannan
Kurunkus: Danjuma Goje ya raba gardama kan batun ficewa daga APC zuwa wata jam'iyya
Ya koma Norway yana da shekaru 8
Bayan Jamus ta miƙa wuya ga ƙasashen ƙawance a Yaƙin Duniya na Biyu, Harald mai shekaru takwas ya koma Norway tare da sauran ’yan gidan sarautar a ranar 7 ga Yuni 1945. Dubban mutane sun taru a titunan Oslo domin tarbarsa da sauran ’yan gidan sarautar.
Domin ƙarfafa alaƙar gidan sarauta da talakawan Norway da kuma sauya tsarin masarautar zuwa na zamani, Harald ya halarci makarantar gwamnati tun yana yaro.
Ya kammala karatunsa na sakandare a Oslo Cathedral School, kafin ya yi aikin soja na tilas na shekara guda a makarantar horas da jami’an rundunar sojin doki ta Norway.
Daga baya ya yi karatun kimiyyar zamantakewa, tarihi da tattalin arziki a Jami’ar Oxford da ke Birtaniya.

Source: Getty Images
Tsohon alkalin Kotun Koli ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa an shiga jimami sakamakon rasuwar tsohon Alkalin Kotun Ƙoli, Mai Shari’a Umaru Atu Kalgo, JSC, CON.
Marigayin, wanda ya kasance fitaccen masani kan shari’a kuma dattijon ƙasa, ya rasu ne da misalin ƙarfe 3:00 na safiyar Talata, 25 ga watan Agustan 2026 bayan fama da doguwar rashin lafiya.
Asali: Legit.ng

