Nyimba Iguru IV: Sarkin da Ya Hau Gadon Sarauta Yana Shekara 3 a Duniya Ya Rasu
- Sarki mafi ƙarancin shekaru a duniya lokacin da aka naɗa shi, ya riga mu gidan gaskiya yana shekaru 34
- Calvin Armstrong Rwomiire Akiiki ya sanar da mutuwar Sarki Oyo Nyimba Kabamba Iguru IV na Uganda
- An naɗa shi sarauta ne yana ɗan shekara uku kacal a duniya bayan rasuwar mahaifinsa tun a 1995
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Uganda - Oyo Nyimba Kabamba Iguru Rukidi IV ya riga mu gidan gaskiya, yanzu haka ana makoki a kauyensa a kasar Uganda.
Mai martaba Oyo Nyimba Kabamba Iguru Rukidi IV ya kafa tarihi ne lokacin da ya zama sarki a 1995 lokacin yana mai shekara uku.

Source: Getty Images
Rahoto ya fito daga BBC cewa sarkin wanda ya taba zama basarake mafi karancin shekaru a duniya ya rasu yana ‘dan shekara 34.
Marigayin yana sarauta ne a can kasar Tooro da ke yammacin kasar Uganda, ya kuma shafe shekaru kusan 30 yana kan karagar mulki.
Masarautar Tooro da ke kan iyakar Uganda da Kasar Jamhuriyyar Congo ba ta sanar da rasuwar ba, amma an ji labari daga gwamnati.
Wani babban jami'i aka rahoto a gidan rediyo ya sanar da rasuwar sarkin, yake cewa ya yi fama da mummunan rashin lafiya kafin ya rasu.
Karin bayani kan Nyimba Kabamba Iguru Rukidi IV
Oyo Nyimba Kabamba Iguru Rukidi IV wanda aka haifa a 1992 ya yi jinya ne a wani asibiti a Amurka.
Marigayi sarkin shi ne basarake na 13 a kasar Tooro wanda aka kafa a wannan karni kuma ya mulki mutane miliyan biyu a karkashinsa.
Duk da Uganda tana karkashin shugban kasa ne a mulkin farar hula, kasar tana da sarakuna da-dama masu tarihi amma marasa iko.
Sanarwar mutuwar Sarki Nyimba Kabamba Rukidi IV
Tashar Sky News tace Calvin Armstrong Rwomiire Akiiki ya sanar da duniya masarauta da mutane sun yi rashi da ba zai misaltu ba.
Calvin Armstrong Rwomiire Akiiki ya yi kira ga mutanen Tooro su hada-kai kuma su kwantar da hankalinsu a lokacin da ake makoki.

Kara karanta wannan
Wani mutumi ya zare bindiga, ya buɗe wa mutane wuta a wurin bikin aure a jihar Kano
Firayim ministan ya kuma bukaci jama’a su dukufu da addu’a Ubangiji ya ji kan sarkin.
Masarautar ta saba zaben sarki ne ta hanyar gado, sai dai Kabamba Iguru Rukidi har ya mutu bai taba aure ba, bai bar wani magaji ba.

Source: Getty Images
Tarihin da sarkin ya bari a kasar Toore
Da aka zabe shi ya hau gadon sarauta a 1995, yana karamin yaro don haka ba a yi bikin nadinsa ba sai lokacin da ya kai shekara 18 a duniya.
A zamaninsa ya wayar da kan talakawansa a kan sha’anin ilmi, sauyin yanayi, samar da aiki da kuma fadakarwa a kan cutar kanjamau.
Shugaban Uganda yana cikin mafi dadewa a mulki
A wani rahoto, mun kawo jerin shugabannin kasashen Afrika da suka fi kowa dadewa a karagar mulki kuma suka haura shekaru 70 da haihuwa.
Daga cikin shugabannin har da Paul Biya na Kamaru, Yoweri Museveni na Uganda da kuma Theodor Obiang Nguema na Equatorial Guinea.
Yawancin wadannan shugabanni sun shafe tsawon shekaru 15 zuwa sama da shekaru 45 suna jan ragamar kasashensu duk da adawar jama'a/
Asali: Legit.ng
