Bayan Kwace Kadarori 48, EFCC na Shirin Sake Dura kan Abubakar Malami

Bayan Kwace Kadarori 48, EFCC na Shirin Sake Dura kan Abubakar Malami

  • EFCC ta ce za ta daukaka ƙara kan hukuncin kotu da ya yi watsi da buƙatarta ta kwace kadarori tara da ake dangantawa da Abubakar Malami
  • Shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ya ce EFCC ta gano kadarori 57 da ake dangantawa da tsohon AGF, inda aka riga aka kammala kwace 48
  • Kotun Tarayya ta ce EFCC ta tabbatar da kadarori 48 a matsayin abin da ake zargin an samu ta haramtacciyar hanya, amma ta ƙi kwace wasu tara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birtaniya - Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC), Ola Olukoyede, ya yi magana kan kwace kadarorin Abubakar Malami.

Ola Olukoyede ya bayyana cewa hukumar za ta daukaka ƙara kan hukuncin kotu da ya yi watsi da buƙatarta ta kwace kadarori tara da ake dangantawa da tsohon Antoni-Janar din na Tarayya.

Kara karanta wannan

EFCC ta yi tayin lada ga masu kwarmato game da dukiyoyin Najeriya da aka wawure

EFCC na son kwace wasu kadarorin Malami
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede da Abubakar Malami Hoto: EFCC Nigeria, Abubakar Malami SAN
Source: Facebook

Jaridar TheCable ta ce Olukoyede ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 26 ga watan Agustan 2026 yayin gabatar da lacca a taron 43 na Cambridge International Symposium on Economic Crime a Jesus College, Jami’ar Cambridge da ke Birtaniya.

An gano kadarori 57 a hannun Malami

Shugaban EFCC ya ce hukumar ta fara bincike kan Malami ne bayan samun zargin da ta bayyana a matsayin shakkun cin zarafin ofishi.

Ya ce a cikin shekaru takwas da Malami ya yi a matsayin AGF, EFCC ta gano kadarori 57 da ake dangantawa da shi, kuma kotu ta riga ta amince da kwace kadarori 48 daga cikinsu.

“Mun gano cewa cikin shekaru takwas da ya yi yana kan mukaminsa, mun iya gano kadarori kusan 57 da ake dangantawa da shi. Mun samu damar kwace 48,” in ji Olukoyede.

Ya ƙara da cewa hukumar tana shirin daukaka ƙara domin neman kwace sauran kadarori tara, The Punch ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta sake gano lam'a a shirin Atiku na dawo da tallafin fetur

“Ko waɗannan tara da aka bar masa, ina la’akari da shigar da ƙara domin mu kwace komai daga gare shi. Kuma za mu yi hakan,” in ji shi.

Abin da kotun ta yanke

Wannan bayani na EFCC ya zo ne makonni bayan da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin kwace kadarori 48 da ake dangantawa da tsohon AGF.

Da farko, an sanya kadarorin 57 ƙarƙashin umarnin wucin-gadi na kwacewa a watan Janairu.

A hukuncin da kotun ta yanke ranar 15 ga Yuli, ta ce EFCC ta tabbatar da cewa kadarori 48 ɗin sun kasance abin da ake zargin an samu daga haramtattun ayyuka.

Sai dai Alƙali Joyce Abdulmalik ta yi watsi da buƙatar hukumar kan wasu kadarori tara da ke Kebbi da Kaduna.

Kotun ta ce EFCC ba ta samu damar tabbatar da cewa an samo waɗannan kadarorin ta hanyar da ta saba wa doka ba.

EFCC za ta daukaka kara kan kadarorin Malami
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede Hoto: @OfficialEFCC
Source: Twitter

Malami​ ya kafa kwamitin kamfen

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya kaddamar da Darakta-Janar da sama da mambobi 600 na kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar ADC a Jihar Kebbi.

Malami ya buƙaci mambobin kwamitin su gina haɗaɗɗiyar jam’iyyar siyasa mai ƙarfi wadda za ta isa ga al’ummomi daban-daban a faɗin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng