Shugaban Jam'iyyar APC Ya Fadi Ya Mutu ana Tsaka da Taron Sulhu

Shugaban Jam'iyyar APC Ya Fadi Ya Mutu ana Tsaka da Taron Sulhu

  • Shugaban APC a Ijumu, Oyewole Mayowa Solomon, ya rasu bayan ya fadi a yayin taron sasanta rikicin jam’iyyar da aka gudanar a Iyara
  • An garzaya da Solomon zuwa asibiti a Kabba bayan an ba shi agajin gaggawa, inda aka tabbatar da rasuwarsa
  • Sanata Sunday Karimi da Hon. Salman Idris sun bayyana rasuwar shugaban jam’iyyar a matsayin babban rashi ga APC a Ijumu da jihar Kogi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kogi - Shugaban jam’iyyar APC mai mulki na karamar hukumar Ijumu ta jihar Kogi, Oyewole Mayowa Solomon, ya yi bankwana da duniya.

Marigayjn ya rasu ne bayan ya yanke jiki ya fadi a lokacin da ake gudanar da wani taron sasanta rikicin jam’iyyar a ranar Juma’a, 21 ga watan Agustan 2026.

Shugaban APC ya mutu a Kogi
Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: Prof Nentawe Yilwatda
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce Solomon ya fadi ne yayin taron da aka gudanar a​ Iyara, hedikwatar karamar hukumar Ijumu.

Kara karanta wannan

Rasuwar babban jigon APC a Kano ta taɓa Shugaba Tinubu ana shirin fara kamfen 2027

An ba shi agajin gaggawa a wurin taron kafin a tafi da shi zuwa wani asibiti da ke Kabba, inda aka tabbatar da cewa ya rasu kafin isowarsa.

An shirya taron domin sulhu

Tsohon shugaban karamar hukumar Ijumu, Funsho Olumoko, ne ya shirya taron domin sasanta bangarorin jam’iyyar, warware sabanin cikin gida da kuma karfafa hadin kai tsakanin masu ruwa da tsaki gabanin wasu harkokin siyasa da za su gudana nan gaba.

Sai dai an samu labarin cewa taron da ya gabata ya kare ba tare da cimma matsaya ba sakamakon wani zargin rikici da ya dabaibaye shugabancin jam’iyyar a karamar hukumar.

Wannan ne ya sa marigayi Solomon da wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da manyan jami’an gwamnati suka fice daga wurin taron.

An ce taron da aka sake gudanarwa a ranar Juma’a an shirya shi ne domin rage rarrabuwar kawuna ta hanyar hada wasu zababbun shugabannin siyasa, shugabannin karamar hukuma da na mazabu, shugabannin mata da matasa, da kuma wadanda gwamnati ta nada daga dukkan mazabu 15 na Ijumu.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da zaman sulhu na siyasa, shugaban APC ya faɗi ƙasa matacce

Sanatoci sun yi jimamin rasuwa

A halin da ake ciki, ’yan majalisar tarayya da ke wakiltar yankin, Sanata Sunday Karimi mai wakiltar mazabar sanatan Kogi ta Yamma, da Hon. Salman Idris mai wakiltar mazabar Kabba-Bunu/Ijumu a Majalisar Wakilai, sun bayyana matukar alhini kan rasuwar shugaban jam’iyyar.

Sun bayyana marigayin a matsayin mutum mai biyayya da jajircewa, kuma mai iya hada kan jama’a a matakin kasa, tare da cewa za a yi matukar kewar gudunmawar da ya bayar wajen bunkasar APC a Ijumu da Kogi ta Yamma.

Shugaban APC a Kogi ya bar duniya
Taswirar jihar Kogi, tarayyar Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kogi, ASP Saliu Oyiza Afusat, bai mayar da martani kan tambayar da aka aika masa game da lamarin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Sanatan da ya bar APC ya samu tikitin PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Saliu Mustapha mai wakiltar Kwara ta Tsakiya ya karɓi tikitin PDP domin neman kujerar sanata a zaɓen 2027.

Ya karbi tikitin ne bayan ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar mai mulki sakamakon doguwar rashin jituwa tsakaninsa da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng