Yan Bindiga Sun Bude Wuta, Sun Kashe Malamin Addinin Musulunci a Najeriya
- ‘Yan bindiga sun kai hari kauyen Gidan Kare, inda suka kashe malamin addinin Musulunci tare da yin garkuwa da akalla mutane 10
- Mazauna sun ce ‘yan bindigar sun shirya harin ne bayan sun lura da yadda mutanen kauyen ke komawa Tureta da safe
- Mutanen yankin sun yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro su kara daukar matakan dakile hare-haren ‘yan bindiga a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto, Nigeria - Akalla mutane 10 ne aka yi garkuwa da su, yayin da aka kashe wani malamin addinin Musulunci bayan ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Gidan Kare da ke karamar hukumar Tureta a jihar Sokoto.
Maharan sun kutsa cikin kauyen da misalin karfe 8:00 na safiyat ranar Alhamis, bayan da mazauna kauyen suka dawo daga garin Tureta, inda da dama daga cikinsu ke kwana domin tsira daga hare-haren ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun kai harin ta'addanci bayan gwamnati ta bayar da tallafin kudi a Sokoto

Source: Original
Yan bindiga sun bude wa mutane wuta
Wani mazaunin kauyen ya shaida wa Daily Trust cewa maharan sun bude wa mutanen kauyen wuta, inda suka kashe mutum daya, suka jikkata wani, sannan suka yi garkuwa da wasu 10.
Mutumin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce
“Yawanci mutanen kauyenmu suna tafiya su kwana a garin Tureta domin kauce wa hare-hare da farmakin ‘yan bindiga. Da safe ne suke komawa gidajensu.
“Amma yau, da mutanen kauyen suka dawo, sai yan bindigar suka shigo suka fara harbe-harbe ba kakkautawa. Sun harbe mutum daya ya mutu, suka jikkata wani, sannan suka yi garkuwa da mutane 10."
Daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su akwai Mallam Dan Manga, Shehu, tagwayen mata Hassana da Hussaina, Badaru, ‘ya’yan Mallam Ayuba guda biyu, Saratu da wasu mutum biyu.
An kashe malamin addinin musulunci
Mazaunin ya ce ya halarci jana’izar wani malamin addinin Musulunci, Mallam Abubakar Danjimme, a garin Tureta da yammacin Alhamis, bayan an kashe shi a harin.
Sai dai ya ce akwai fargabar cewa wasu mutane na iya kasancewa sun bace, yayin da har yanzu ba a san inda suke ba.
Wani mazaunin Daddade, wata al’umma da ke kusa da Gidan Kare, ya ce marigayi Mallam Abubakar shi ne malamin addinin Musulunci da ya koyar da shi.
Ya kara da cewa maharan sun kuma shiga kauyukan Daddade da Janwake, amma ba su samu mutane ba, saboda da dama daga cikinsu sun gudu daga gidajensu sakamakon rashin tsaro.
Ana zargin yan bindiga sun tsara harin
Wani mazaunin garin Tureta, wanda ke ba mutanen Gidan Kare da sauran kauyukan da hare-hare suka raba da muhallansu masauki, ya bayyana yadda mutanen kauyen ke zuwa Tureta su kwana sannan su koma gidajensu kowace safiya.
Ya ce yadda maharan suka kai harin ya nuna cewa sun dade suna lura da yadda mutanen kauyen ke tafiya da dawowa, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Source: Facebook
kara da cewa daya daga cikin matan da aka yi garkuwa da su ‘yar uwar kawunsa ce.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai, ya ce zai tuntubi jami’in ‘yan sanda na yankin Tureta domin samun cikakken bayani kan lamarin.

Kara karanta wannan
Surutun jama’a da mantawa da wasu ya jawo an janye sunayen kwamitin kamfen Tinubu
An kashe yan bindiga a Sakkwato
A wani labarin, an ji cewa sojoji da yan sanda sun yi nasarar dakile harin da yan bindiga suka yi yunkurin kai wa barikin sojoji a jihar Sakkwato.
Dakarun tsaron Najeriya sun kashe da dama daga cikin maharan yayin da sauran suka tsere cikin daji don tsira da rayukansu.
Asali: Legit.ng
