Maulidin Annabi SAW: Sanusi II Zai Hawa na domin Soyayya ga Fiyayyen Halitta
- Mai Martaba Sarkin Kano Khalifa Dr. Muhammadu Sanusi II, CON, zai yi hawa na musamman domin nuna farin ciki da murnar watan Mauludi
- Wannan sanarwar ta ce za a gudanar da hawan ne domin kara bayyana irin soyayyar da al’ummar Kano ke yi wa Annabi Muhammad SAW
- Masoya Annabi ﷺ sun bayyana farin cikinsu kan hawan, tare da addu’ar Allah Ya ci gaba da ba Sarkin Kano lafiya, hikima da daukaka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Mai Martaba Sarkin Kano Khalifa Dr. Muhammadu Sanusi II, PhD, CON, ya shirya yin hawa na musamman a jihar Kano.
Basaraken zai yi hawa na musamman domin nuna murna da farin ciki a cikin wannan wata mai albarka, watan da aka samu fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW.

Source: Twitter
Wakilin Legit Hausa ya samu wannan bayani ne daga shafin Masarautar Kano da ke yawan kawo muhimman bayanai game da basaraken a X.
Sanarwar ta bukaci al’ummar Kano da su fito cikin farin ciki da murna, domin yin tarayya da Mai Martaba Sarkin Kano a wannan hawa na musamman.
Ta ce hawan zai kasance wani muhimmin al’amari da zai kara tabbatar da kimar Kano da kuma irin soyayyar da al’ummar jihar ke da ita ga Manzon Allah SAW.
Sanarwar ta bayyana cewa kowa ya san Kano da shahara wajen nuna soyayya ga Annabi Muhammad SAW, musamman a lokacin da ake gudanar da bukukuwan Mauludi.
Sanarwar ta ce:
"Mai Martaba Sarkin Kano Khalifa Dr. Muhammadu Sanusi II, PhD, CON, zai yi hawa domin nuna murna da farin ciki a cikin wannan wata mai albarka, watan da aka samu fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW.
Saboda haka, mu fito cikin farin ciki da murna, mu yi tarayya da Mai Martaba a wannan hawa na musamman, domin wani muhimmin al’amari da zai kara tabbatar da kimar Kano da irin soyayyar da take da ita ga Manzon Allah SAW wadda kowa ya san Kano ta shahara da ita."
Yadda hawan Sanusi II zai yi tasiri
Masoya Annabi SAW sun ce za su yi matukar farin ciki da hawan da Mai Martaba Sarkin Kano Khalifa Dr. Muhammadu Sanusi II zai yi a Kano.
Sun kuma bayyana fatan cewa Allah Ya sanya wannan al’ada ta ci gaba da gudana duk shekara da yar Allah Madaukakin Sarki.
Masu shirya taron sun yi addu’ar Allah Ya kara wa Mai Martaba Sarkin Kano lafiya, hikima da daukaka, tare da raya Kano cikin soyayya da biyayya ga Manzon Allah.
Sakon Tinubu ga masu Maulidi a Najeriya
A wani labarin, an ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya daukacin musulmi zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW.
Tinubu ya bukaci Musulmi su yi koyi da sadaukarwa, hakuri, juriya da tawali’u na fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW.
Shugaban ya bukaci ’yan Najeriya su yi addu’ar kawo karshen rashin tsaro tare da taimakon marasa karfi a wannan lokaci.
Asali: Legit.ng

