Tsare El Rufai: Jigo a ADC Ya Aika da Muhimmin Sako ga Dattawan Arewa

Tsare El Rufai: Jigo a ADC Ya Aika da Muhimmin Sako ga Dattawan Arewa

  • Jafaru Ibrahim Sani ya bukaci dattawan Arewa da shugabannin siyasa su duba batun Nasir El-Rufai ba tare da bambancin siyasa ba
  • Tsohon mataimakin shugaban ADC na shiyyar Arewa maso Yamma ya ce adalci da bin ka’ida su zama ginshikin yadda ake tunkarar lamarin tsohon gwamnan Kaduna
  • Jafaru Sani ya ce halin da El-Rufai ke ciki ya kamata ya sa Arewa ta yi tunani kan irin siyasar da take ginawa ga al'umma masu zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ADC na shiyyar Arewa maso Yamma, Mallam Jafar Ibrahim Sani, ya aika da sako ga dattawan Arewa kan ci gaba da tsare Nasir El-Rufai.

Jafaru Sani ya bukaci dattawan Arewa da shugabannin siyasa su yi watsi da bambance-bambancen siyasa, su tabbatar da adalci da bin ka’ida a kan lamarin da ya shafi tsohon gwamnan na jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Danjuma Goje ya raba gardama kan batun ficewa daga APC zuwa wata jam'iyya

Jafaru Sani ya yi magana kan tsare El-Rufai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai Hoto: Bello El-Rufai
Source: Facebook

Jafaru Sani ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken El-Rufai, The North, Our Elders and the Test of Loyalty, da ya sanya a shafinsa na X ranar Litinin, 24 ga watan Agustan 2026.

Me jigon ADC ya ce kan El-Rufai?

Jigon na ADC ya ce halin da tsohon gwamnan ke ciki ya kamata ya sa a yi tunani kan irin al’adar siyasa da ake ginawa domin al'umma masu zuwa.

Ya ce alakar siyasa na kara zama ta anfani ne kawai, inda wasu ke nuna biyayya muddin suna amfana, amma su yi watsi da abokan siyasarsu idan suka shiga mawuyacin hali.

A cewarsa, duk da cewa mutane na iya samun ra’ayoyi daban-daban kan El-Rufai, ba za a iya musanta irin tasirin da ya yi a harkokin gwamnati da rayuwar jama’a a Najeriya ba.

“Saboda haka, abin damuwa ne ganin karancin goyon baya daga wasu daga cikin mutanen da a baya suka kasance mafi kusanci da shi. Lokacin da mutum ya shiga wahala ne biyayya ta fi zama mai muhimmanci,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya

Ya bukaci a yi adalci

Jafaru Sani ya bukaci dattawan Arewa, masu ruwa da tsaki da shugabannin siyasa kada su bari bambancin siyasa ya zama dalilin watsi da adalci da bin ka’ida a lamarin El-Rufai.

Ya ce adalci ya kamata ya kasance ginshikin matakin da za a dauka kan lamarin tsohon gwamnan, ba tare da la’akari da alakar mutum da shi ko sabanin siyasa ba.

“Idan aka yi adalci, hakan ya kamata ya kai ga duk wani sakamako da doka da kotuna za su tabbatar, ciki har da sakin Mallam El-Rufai bisa doka idan hakan ya dace,” in ji shi.

Ya kare El-Rufai kan kalaman da ya taba yi

Da yake magana kan kalaman El-Rufai game da dattawan Arewa, Jafaru Sani ya ce tsohon gwamnan bai nuna cewa Arewa ba ta da dattawa, malamai, sarakunan gargajiya ko shugabannin da suka kware ba.

Jafaru Sani ya ce Arewa ta cancanci samun ingantacciyar rayuwa, wadata ga ‘ya’yanta da kuma matsayi mai karfi a duniya.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa 6, malaman addini 500 sun bayyana dan takarar shugaban kasarsu a 2027

Ya jaddada cewa cimma wadannan manufofi na bukatar yin nazari na gaskiya da kuma daukar matakin da ya dace.

Jafaru Sani ya ba dattawan Arewa shawara
Jigo a jam'iyyar ADC, Mallam Jafaru Sani Hoto: @JafaruSani01
Source: Twitter

El-Rufai ya maka ICPC kara kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Nasir El-Rufai, ya shigar da sabuwar ƙarar N10bn kan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifuka (ICPC).

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya garzaya kotu ne bisa zargin cewa jami'an hukumar sun hana matarsa da ɗansa damar ganinsa yayin da yake tsare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng