Yadda Aka Yi Jana'izar Sarkin Gumel cikin Jimami, Kashim da Manyan Kasa Sun Halarta
- Dubban al’ummar Gumel da wasu sassan Najeriya sun taru a Juma’a domin halartar sallar jana’izar marigayi Sarkin Gumel
- Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da Gwamnan Jigawa Umar Namadi, sarakuna da manyan ’yan siyasa sun halarci jana’izar
- Marigayi sarkin, wanda ya rasu yana da shekaru 85 a Alkahira, ya bar ’ya’ya 33, maza 21 da mata 12, da jikoki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gumel, Jigawa - Dubban masu makoki, sarakunan gargajiya, ’yan siyasa da manyan baki daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen makwabta sun taru a Gumel, Jigawa, ranar Juma’a.
Sun taru ne domin halartar sallar jana’izar marigayi Sarkin Gumel, Alhaji Ahmad Muhammad Sani II, wanda ya rasu yana da shekaru 85.

Source: Facebook
Yadda aka yi jana'izar Sarkin Gumel
An gudanar da sallar jana’izar ne a fadar marigayi sarkin da ke Masarautar Gumel, a yammacin Juma’a, 4 ga Satumba, 2026, bayan rasuwarsa a birnin Alkahira na ƙasar Masar, cewar Daily Trust.
Marigayi Sarkin ya rasu ne ranar Alhamis, 3 ga Satumba, bayan fama da rashin lafiya na wani lokaci, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
An haifi marigayi Sarkin a shekarar 1942, kuma ya shafe shekaru masu yawa yana jagorantar al’ummar masarautar tare da kare al’adunta, tarihinta da kyawawan dabi’unta.
Jana’izar ta samu halartar manyan mutane da dama, ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya jagoranci tawagar fadar shugaban ƙasa zuwa Gumel.

Source: Facebook
Gwamnonin da suka halarci jana'izar Sarkin Gumel
Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi, shi ma ya halarci jana’izar tare da sauran manyan jami’an gwamnati da ’yan siyasa.
Gwamnonin Kano da wasu jihohin Arewa su ma sun halarci jana’izar domin nuna girmamawa ga marigayi sarkin da iyalansa.
Manyan ’yan siyasa, jami’an gwamnati da sarakunan gargajiya, ciki har da sarakunan Kano, Jigawa da sauran manyan baki daga sassa daban-daban na ƙasar, sun halarci jana’izar.
An ce garin Gumel ya cika da masu makoki, yayin da mazauna garin da baƙi suka yi cincirindo a masarautar domin yi wa marigayi sarkin bankwana na ƙarshe.
Marigayi Sarkin Gumel ya rasu ya bar ’ya’ya kusan 33, ciki har da maza 21 da mata 12, baya ga dimbin jikoki.
Da yake jawabi yayin jana’izar, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya roƙi Allah Ya gafarta wa marigayi sarkin, Ya ba shi hutu na har abada, Ya kuma saka masa da alherin ayyukansa, cewar Leadership.
Shettima ya kuma roƙi Allah Ya bai wa iyalan marigayi sarkin, al’ummar Masarautar Gumel da gwamnatin Jigawa ƙarfin hali da haƙurin jure wannan babban rashi.
Gwamna Namadi ya yi jimamin rasuwar Sarkin Gumel
An ji cewa Gwamna Umar Namadi ya bayyana rasuwar Sarkin Gumel, Alhaji Dr Ahmed Muhammad Sani II, a matsayin babban rashi ga jihar Jigawa.
Rahotanni sun ce Sarkin ya rasu yana da shekara 82 a birnin Alkahira na kasar Masar bayan gajeriyar rashin lafiya.
Marigayin ya shafe sama da shekaru 45 yana sarautar Gumel, inda ya ba da gudunmawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaba.
Asali: Legit.ng

