Kasar da ake ba da Tallafin Kusan Naira Miliyan 100 idan aka Haifi Yaro 1
- Gwamnatin Singapore ta sanar da sabon tsarin tallafi da zai bai wa kowane yaro da ya cancanta tallafin gwamnati da ya kai kwatankwacin N94m
- Firaministan Singapore, Lawrence Wong, ya ce sabon tsarin zai saukaka hanyoyin tallafa wa iyalai tare da tabbatar da cewa kowane yaro ya samu tallafin
- An ce shirin zai amfani sama da yara 610,000 daga gidaje kusan 380,000, domin karfafa gwiwar iyalai su kara haihuwa yayin da ake fuskantar raguwar haihuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Singapore – Gwamnatin Singapore ta sanar da wani sabon kunshin tallafi da zai bai wa kowane yaro dan kasar da ya cancanta tallafin gwamnati da zai kai kusan kudin Singapore 70,000, kwatankwacin N94m.
Firaministan kasar, Lawrence Wong, ya bayyana sabon shirin yayin jawabinsa na a wani taro a ranar 23 ga watan Agustan 2026.

Source: Getty Images
Bloomberg ta wallafa cewa an bayyana cewa sabon tsarin zai bai wa iyalai tallafi tun daga haihuwar yaro har zuwa lokacin da zai kai shekaru 17 da haihuwa.
Kudin haihuwa da ake bayarwa
Lawrence Wong ya ce gwamnatin kasar ta shirya samar da tallafin farko na kudin Singapore 62,000 a karkashin sabon tsarin.
Kunshin ya kunshi dala Singapore 10,000 a matsayin kyauta ga yaro, dala 32,000 na sayen abubuwa da kuma dala 5,000 na tallafin na tallafi.
Haka kuma, gwamnati za ta rika kara bayar da gudunmawa har zuwa dalar Singapore 5,000 a asusun CDA, tare da kara dala Singapore 10,000 a asusun karatun yaro bayan sakandare.
Wong ya ce idan aka hada sabon tsarin da sauran tallafin da gwamnatin kasar ke bayarwa, jimillar tallafin da kowane yaro zai samu za ta kai kusan dala Singapore 70,000.
Yadda Singapore za ta raba tallafin
A cewar gwamnatin, za a biya tallafin kudin Singapore 10,000 sau biyu a cikin shekarar farko bayan haihuwar yaro.

Kara karanta wannan
Jigo a APC kuma dan kasuwar mai ya kwancewa Atiku zani kan dawo da tallafin fetur
Haka kuma, yaro zai rika samun kudin Singapore 2,000 duk shekara daga shekara daya zuwa lokacin da zai kai shekaru 16.
Da zarar yaron ya kai shekaru 17, gwamnati za ta kara masa kudin Singapore 10,000 a asusun da aka ware domin ci gaba da karatunsa.
Ya ce tsarin da ake amfani da shi a baya ya yi matukar rikitarwa, lamarin da ya sanya wasu iyaye wahala wajen fahimtar irin tallafin da suka cancanta.
Dalilin raba kudin haihuwa
Rahotanni sun nuna cewa an ce sabon tsarin zai amfani sama da yara 610,000 daga gidaje kusan 380,000 a fadin Singapore.
Matakin wani bangare ne na kokarin gwamnatin kasar na karfafa wa mutane gwiwar kara haihuwa yayin da Singapore ke fuskantar raguwar yawan haihuwa.

Source: Getty Images
Business Today Malaysia ta rahoto Lawrence Wong ya ce gwamnati na zuba jari mai yawa wajen tallafa wa iyalai da 'yan kasar a matakai daban-daban na rayuwa.
Yarjejeniyar Ronaldo da Georgina
A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa fitaccen dan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo da abokiyar zamansa, Georgina Rodríguez, sun kulla wata yarjejeniyar mallakar kadarori kafin aurensu.
Rahotanni sun ce yarjejeniyar ta tanadi cewa kadarorin da kowannensu ya mallaka kafin aure za su ci gaba da kasancewa karkashin mallakar mutum daya bayan da suka yi aure.
An ce ma'auratan sun sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ranar 10 ga watan Agusta, kwana daya kafin rahotannin da suka ce sun gudanar da wani karamin bikin aure a birnin Lisbon na kasar Portugal.
Asali: Legit.ng

