Musulmi Sun Yi Rashi a Arewa, Babban Limami Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Al’ummar Musulmi a Alfeti a Ankpa ta sanar da rasuwar Sheikh Mustapha Kamal Ahmad, babban limamin garin
- Marigayin ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada ilimin Musulunci da jagorantar al’umma, yayin da dalibai da mabiyansa ke yi masa addu'a
- Sanusi Abdul Sanusi ya bayyana rasuwar Sheikh Ahmad a matsayin babban rashi ga iyalansa, al’ummar Musulmi da yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ankpa, Kogi - Al’ummar Musulmi a Alfeti, wani kauye da ke karamar hukumar Ankpa ta Kogi, na jimamin rasuwar Sheikh Mustapha Kamal Ahmad.
Al'ummar Musulmi a yankin sun bayyana jimami bayan samun labarin rasuwar malamin inda suka ce mutum ne mai son addini.

Source: Facebook
An yi rashin babban malamin Musulunci
Wakilin Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga shafin Ummah Idah TV wanda aka wallafa a Facebook.
Sheikh Ahmad ya kasance babban limamin garin Alfeti, kuma al’umma ta sanar da rasuwarsa cikin wata sanarwar ta’aziyya da aka fitar ranar Laraba, 19 ga Agusta, 2026.
Al’ummar Musulmi ta bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi da ya shafi daukacin jama'ar yankin, musamman mutanen da suka amfana da iliminsa da jagorancinsa
Gudunmawar Sheikh Mustapha Kamal Ahmad
A cikin sanarwar, al’umma ta bayyana cewa Sheikh Ahmad ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada addinin Musulunci da koyar da ilimin addini ga Musulmi a Alfeti da yankunan da ke kusa.
Dalibansa, mabiyansa da sauran al’ummar Musulmi sun kasance cikin wadanda za su ci gaba da tunawa da gudummawar da marigayin ya bayar wajen koyarwa da hidima ga addini da bil’adama.
Al’umma ta ce rayuwarsa ta kasance abin koyi wajen neman ilimi, imani, koyarwa da kuma bautar al’umma, musamman ta fuskar jagoranci da nasiha.
Ta kuma bayyana cewa gudummawar da ya bayar a matsayin malamin addini da jagoran al’umma ta bar babban tarihi ga mutanen da suka samu damar kasancewa karkashin jagorancinsa.

Kara karanta wannan
Abubuwan da ya dace a sani game da yarjejeniyar da aka yi tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya

Source: Original
An yi wa Sheikh Ahmad addu’a
Bayan sanar da rasuwarsa, al’ummar ta yi addu’ar Allah Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya karbi kyawawan ayyukansa, sannan Ya ba shi matsayi mafi girma a Aljanna
An kuma roki Allah Ya haskaka kabarinsa, Ya yalwata masa, sannan Ya bai wa iyalansa, dalibansa da mabiyansa hakurin jure wannan babban rashi
Sanusi Abdul Sanusi, wani fitaccen dan asalin Ankpa kuma dan kasuwa, ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi ga iyalansa da al’ummar Musulmi
Sanusi ya ce rasuwar Sheikh Mustapha Kamal Ahmad ta shafi dukkan wadanda suka amfana da shawarwarinsa, addu’o’insa da zurfin fahimtarsa kan addinin Musulunci
A cikin sakon ta’aziyyarsa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sanusi ya bayyana cewa yana jimamin rasuwar babban limamin Alfeti cikin bakin ciki da tausayi
An yi rashin malamin Musulunci a Gombe
An ji cewa Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana jimami bayan rasuwar malamin Musulunci, yana cewa sun yi rashin mutum mai daraja daga Gombe.
Pantami ya bayyana marigayin a matsayin mahaddacin Alƙur’ani, wanda ya yi karatu a Jami’ar Madina, sannan ya kasance masani kan tarihin magabata.
Ya kuma tuna kyakkyawar mu’amalarsu da ta shafe shekaru 32, inda ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa Aliyu Ladan, Ya shigar da shi Aljannatul Firdaus.
Asali: Legit.ng

