Ana tsaka da Zaman Sulhu na Siyasa, Shugaban APC Ya Faɗi Ƙasa Matacce

Ana tsaka da Zaman Sulhu na Siyasa, Shugaban APC Ya Faɗi Ƙasa Matacce

  • Wani shugaban APC na matakin ƙaramar hukuma a Kogi ya rasu bayan ya fadi yayin taron sulhu da ake yi
  • An garzaya da marigayin zuwa wani asibiti a Kabba bayan kokarin farfado da shi, amma rahotanni sun ce ya rasu jim kadan bayan isarsa
  • Taron na neman kawo hadin kai tsakanin ’yan APC da warware sabanin cikin gida yayin da jam’iyyar ke shirin babban zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ijumu, Kogi - Shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Ijumu a Kogi, Oyewole Mayowa Solomon, ya rasu.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne bayan ya fadi yayin wani taron sulhu a Iyara, hedkwatar karamar hukumar.

Wani shugaban APC ya mutu a taro
Shugaban APC a Najeriya, Nentawe Yitwalda da wasu mambobin jam'iyyar. Hoto: Prof. Nentawe Yitwalda.
Source: Twitter

Lamarin ya faru ne yayin da Solomon ke halartar taron da tsohon shugaban karamar hukumar Ijumu, Funsho Olumoko, ya shirya domin karfafa hadin kai, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Abin da Atiku zai yi don magance rashin tsaro cikin kwana 100 idan ya zama shugaban kasa

Yadda shugaban APC ya mutu a taro

An gudanar da taron a dakin taro na garin Iyara, inda aka hada shugabannin jam’iyya da sauran masu ruwa da tsaki domin warware sabanin da ke tsakaninsu da karfafa hadin kai gabanin ayyukan siyasa masu zuwa.

Majiyoyi a wajen taron sun ce Solomon ya fadi kwatsam yayin da ake gudanar da taron, lamarin da ya jefa mahalarta cikin rudani da firgici.

An ce an yi kokarin farfado da shi kafin daga bisani aka garzaya da shi wani asibiti a Kabba domin samun kulawar likitoci, sai dai rahotanni sun ce ya rasu jim kadan bayan isa asibitin.

Mutuwar tasa kwatsam ta jefa shugabannin jam’iyya, jami’an gwamnati da sauran mahalarta taron cikin alhini da mamaki.

An gudanar da taron ne yayin da masu ruwa da tsaki na APC a Ijumu ke ci gaba da kokarin warware sabanin cikin gida da karfafa hadin kai gabanin babban zaben 2027.

Kara karanta wannan

Tinubu ya dauki sabon mataki kan tsaro, ya ba da wa'adin kwanaki 90

Wani shugaban APC ya rasa ransa a Kogi
Taswirar jihar Kogi da aka yi rashin shugaban APC. Hoto: Legit.
Source: Original

Abin da ya faru a taron jam'iyyar APC

An ce Solomon da wasu jami’an jam’iyyar sun fice daga taron saboda sabanin da ya kunno kai a wajen taron, cewar Punch.

Olumoko, wanda ya shirya taron sulhun ya taba rike mukamin shugaban karamar hukumar kuma ya kasance cikin wadanda ke kokarin hada bangarorin siyasa daban-daban a Ijumu.

Ana sa ran shugabannin siyasa, shugabannin karamar hukuma da na kananan hukumomin zabe, shugabannin mata da matasa, da jami’an gwamnati daga mazabu 15 za su halarci taron.

Ana sa ran mutuwar Solomon za ta yi tasiri kan kokarin sulhunta bangarorin APC a Ijumu, musamman yayin da jam’iyyar ke kara shirye-shiryen babban zaben 2027.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a bayyana a hukumance musabbabin mutuwar Solomon ba, yayin da ake ci gaba da kokarin samun martani daga shugabannin APC.

Tsohon shugaban APC ya mutu a daji

Mun ba ku labarin cewa tsohon shugaban APC daga jihar Kebbi, Alhaji Muhammadu Besse, ya rasa ransa a hannun ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

Yadda dalibin tsangaya ya tsallake rijiya da baya lokacin da abokansa 4 suka rasu a Kano

Majiyoyi sun tabbatar da cewa jigon APC ya mutu a daji bayan shafe makonni da dama a hannun maharan.

Rahotanni sun nuna cewa mutanen biyu da suka bayyana a bidiyon da aka saki daga dajin Birnin Gwari sun mutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.