Yadda aka Cafke Jami'in DSS na Bogi Yana Barazana da Bindigar Karya

Yadda aka Cafke Jami'in DSS na Bogi Yana Barazana da Bindigar Karya

  • Rahotanni sun nuna cewa hukumar DSS ta kama wani mutum mai suna Moferewa Maiye da ake zargi da yin sojan gona a birnin tarayya Abuja
  • An kama Moferewa Maiye ne sanye da kayan aiki irin na DSS tare da bindigar bogi, bayan an zarge shi da tsoratar da masu abubuwan hawa
  • Jami'an tsaro sun bi sawun mutumin har zuwa maboyarsa da ke kusa da kwanar NITEL a Wuse II, Abuja, inda suka cafke shi tare da kayan aikinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar leken asiri ta Najeriya (DSS) ta kama wani mutum mai suna Moferewa Maiye bisa zargin yin kwaikwayon jami'in hukumar da kuma amfani da kayan DSS wajen karbar kudi daga masu abubuwan hawa.

An kama Maiye ne a daren Laraba a maboyarsa da ke kusa da kwanar NITEL, a kan titin Adetokunbo Ademola Way, Wuse II, Abuja.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ɗana tarko, an daƙile harin garkuwa da mutane a Zamfara

DSS na bogi Moferewa Maiye
Moferewa Maiye da ake zargi da zama jami'in DSS na bogi. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa jami'an DSS sun bi sawun mutumin ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan ayyukansa.

An kama shi da kayan DSS

A lokacin da aka kama shi, Maiye yana sanye da kayan aiki na musamman na DSS, sannan yana dauke da bindigar bogi.

Wata majiya mai tushe daga bangaren tsaro ta ce ana zargin mutumin da amfani da kayan da bindigar wajen tsoratar da masu abubuwan hawa da sauran jama'a tare da karbar kudi daga gare su.

Majiyar ta ce:

"Jami'an bincike na kokarin gano tsawon lokacin da wanda ake zargin yake gudanar da irin wadannan ayyukan na kwaikwayon jami'an tsaro da karbar kudi."

Me wanda ake zargin ya fada?

A yayin da ake yi masa tambayoyi, Maiye ya ce ya fito ne daga kauyen Agbajojun da ke karamar hukumar Mopamuro ta jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Yadda motoci suka nutse, komai ya tsaya cak bayan ambaliya a Abuja

Majiyar ta ce wanda ake zargin ya bayyana cewa dan uwansa mai suna Monday Maiye, wanda ya kasance jami'in DSS, ya rasu shekaru da suka gabata.

Rahotn Daily Trust ya nuna cewa ya ce kayan DSS da aka same shi da su mallakar dan uwansa ne marigayin.

Sai dai hukumar DSS na ci gaba da bincike domin gano yadda ya samu kayan hukumar da kuma ko ya dade yana amfani da su wajen aikata irin wannan laifi.

Taswirar birnin tarayya Abuja
Taswirar birnin tarayya Abuja a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

A cewar majiyar, ana kuma binciken ko Maiye yana da alaka da wasu mutane da ke amfani da kayan jami'an tsaro wajen tsoratar da jama'a ko aikata laifuka.

An saki mutanen DSS ta kama

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban DSS, Oluwatosin Adeola Ajayi, ya bayar da umarnin sakin mutane uku da hukumar ta gano cewa an tsare su bisa kuskure.

Mutanen, Umar Ibrahim, Alhaji Bello Rabiu da Jaja Sarki Bamo, an kama su ne a watan Yunin wannan shekara, kafin DSS ta sake duba shari'arsu ta gano cewa ba su da laifi.

Rahotannin da Lgit Hausa ta samu sun nuna cewa DSS ta kuma amince da biyan mutanen ukun Naira miliyan 3 a matsayin diyya saboda tsare su bisa kuskure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng