Musulmai na Ciki Suna Hutawa, Wasu Tsageru Sun Bankawa Masallaci Wuta
- Rundunar 'yan sandan Birtaniya ta fara bincike kan wani hari da aka kai masallacin Peacehaven, kusa da birnin Brighton
- Wannan hari dai ya kara tayar da hankalin al'umma musamman musulmin da ke rayuwa a yankin
- Mai kula da masallacin ya bayyana cewa wannan shi ne hari mafi muni da aka kai masu tun bayan kafa wurin ibadar shekaru hudu da suka wuce
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United Kingdom - Wasu miyagu da ba a san ko su waye ba sun kai hari tare da banka wa masallaci wuta a garin Peacehaven, kusa da birnin Brighton a Kudancin Ingila.
Lamarin ya faru ne a daren ranar Asabar da ta gabata, kuma ana zargin maharan sun kai wannan farmaki ne domin nuna kin jinin musulmi.

Source: Getty Images
Jaridar Tribune Nigeria ta tattaro cewa ’yan sanda Ingilan sun fara bincike kan lamarin, inda suka ce za su dauki harin a matsayin laifin nuna kiyayya ga Musulmi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka banka wa masallaci wuta
A lokacin da lamarin ya faru, mutane biyu suna cikin masallacim, amma sun tsira ba tare da rauni ba.
Rahotanni sun nuna cewa wasu mutum biyu da suka rufe fuskokinsu sun yi ƙoƙarin bude kofar masallacin da karfi kafin, sukanzuba fetur a bakin kofar sannan suka kunna wuta.
Jami’an bada agajin gaggawa na Birtaniya sun isa wurin kafin ƙarfe 10:00 na dare domin dakile gobarar.
Musulmi sun koka kan kona masallacin
An tattaro cewa shugahan kwamitin masallacim da wani masulmi, wadanda sun kai shekaru 60, na ciki suna shan shayi lokacin da suka ji kara kuma wuta ta kama.
Wani mai kula da masallacin wanda ya yi magana da CNN ba tare da bayyana sunansa ba ya ce:
“Ba don Allah ya kare ba, da sun mutu nan take. Wadannan mutanen sun zo ne da niyyar yin mummunar barna, duk mun tsorata, ba mu san me zai biyo baya ba.”
Wane mataki hukumomin Birtaniya suka dauka?
’Yan sanda sun tabbatar da cewa gobarar ta yi babban lahani ga kofar masallacin da kuma wata mota da aka ajiye a waje ta shugaban kwamitin masallacin.
Hukumomi Ingila sun ƙara yawan jami'an tsaro da ke sintiri a fadin Sussex domin kwantar da hankalin mutane.
Dan majalisar wakilai na jam’iyyar Liberal Democrat, James MacCleary, ya yi Allah-wadai da lamarin, inda ya bayyana shi a matsayin “abin kunya."

Source: Getty Images
Masallacin Peacehaven, wanda aka kafa shekaru hudu da suka wuce, ya taba fuskantar kananan hare-hare da suka hada da batanci da barna.
Amma, a cewar mai kula da masallacin, wannan shi ne mafi munin harin da aka kai tun kafuwarsa.
'Yan bindiga sun kai hari masallaci a Zamfara
A wani labarin, kun ji cewa yan bindiga sun kai hari masallaci ana tsakiyar Sallar Asuba a kauyen Yandoto da ke yankin karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan
Tsautsayi: Tankar mai ta yi tsiya a cikin mutane ranar Juma'a, an rasa rayuka da yawa
Rahotanni sun nuna cewa 'yan ta'addan sun kashe mutane yayin da su ke tsakiyar sallah, lamarin da ya tada hankalin mazauna yankin.
Shaidu sun ce yan ta'addan sun kutsa cikin masallacin ana cikin Sallah, suka bude wa masu ibada wuta babu kakkautawa, inda suka kashe mutane biyar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

