"Zan Bayar Da N4.6m": Attajirin Matashi Ya Bayar Cigiyar Tsohon Dutsen Guga, Zai Biya Makuden Kudi

"Zan Bayar Da N4.6m": Attajirin Matashi Ya Bayar Cigiyar Tsohon Dutsen Guga, Zai Biya Makuden Kudi

  • Wani dan kasuwa ya wallafa faifan bidiyo yana neman tsohon dutsen guga na gargajiya don biyan kudi
  • Ya ba da lambar wayarsa ta WhatsApp inda za a same shi idan akwai wanda ya mallaki wannan dutsen gugan
  • Matashin sai dai ya bayyana irin kalan tsohon dutsen gugan da ya ke so, ya na bukatar mai kuran karfe ne

Wani dan kasuwa mai suna @olakanmiegolddeni ya ba da cigiyar tsohon dutsen guga akan zai siya N4.6m a wurin duk wanda ya nemo.

A wani faifan bidiyon da aka yada a TikTok ya nuna irin tsohon dutsen gugan da yake bukata, a cewarsa zai ba da makudan kudade har N4.6m ga duk wanda ya samo dutsen gugan.

Attajiri/Dan kasuwa/Matashi/Dutsen guga
Matashin da ya ba da cigiyar dutsen guga tare da alkawarin zai biya N4.6m. Hoto: @olakanmiegolddrni
Asali: TikTok

Ya kuma ajiya lambar wayarsa ta WhatsApp wanda mutane za su iya amfani da ita don tuntubarsa ta hanyar tura masa sako ba kira ba, musamman idan sun shirya samo dutsen gugan ko kuma suna da shi.

Kara karanta wannan

Garabasa: 'Yan Twitter sun more, Elon Musk zai fara raba musu kudi, amma da sharadi

Amma a cikin bidiyon, matashin ya nuna irin kalan dutsen gugan da yake so, yana bukatan wanda yake iya kama karfe wato jikinsa kaman kuran karfe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

‘’Ku turamin sako idan har kuna da irin wannan dutsen, zan biya makudan kudade, ku turamin sako ta WhatsApp."

Ga bidiyon a kasa:

Mutane da dama sun yi ta maida martani kan cewa ai suna da wannan dutsen guga, tuni suka fara neman yadda kasuwancin zai kullu.

Martinin jama’a a kafar sada zumunta

@iredia_24:

“Kuran karfe a cikin karfe.”

@trippises:

“Nawa za ka siya ina da guda uku na siyarwa.”

@luombier:

“Ina da kusan dubu 10, ka shirya min kudina.”

@sseguyafrancis381:

“Ina da kuran karfen da kanta.”

Budurwa Ta Fashe da Kuka Saboda Rashin Ciniki a Shago, Bidiyon ya Yadu

Kara karanta wannan

“Ina Matukar Kaunarsa Da Dukkan Zuciyata”: Matashiya Ta Wallafa Hotunan Sauyawar Mijinta Mai Nakasa Bayan Shekaru 10

A wani labarin, an gano wata budurwa a wani faifan bidiyo da ta wallafa ta fashe da kuka saboda ta shafe makwanni uku babu ko mutum daya da yazo shagonta ya sayi kaya.

A faifan bidiyon budurwar ta dauki bidiyon tana zagawa cikin shagon ta na sharbar kuka har da majina saboda rashin ciniki, ta tabbatar da cewa ta rage farashin kayanta sosai, ba kamar yadda ya ke a baya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel