Binciken Gaskiya: Alkali Tsammani Ya Nemi Yan Najeriya Su Yafe Wa Tinubu Kan Laifin Safarar Kwaya?

Binciken Gaskiya: Alkali Tsammani Ya Nemi Yan Najeriya Su Yafe Wa Tinubu Kan Laifin Safarar Kwaya?

  • A wani bangare na dalilan shigar da ƙararsu, ƴan adawa sun yi zargin cewa Bola Ahmed Tinubu, bai cancanci tsayawa takara ba
  • Ƴan adawar sun kafa hujja da cewa an ci tarar Tinubu $460,000 saboda laifin da ya shafi rashin gaskiya, wato fataucin miyagun kwayoyi da kotun Amurka ta yi
  • Masu amfani da Facebook da X sun yi iƙirarin cewa alƙali Haruna Tsammani ya ce kamata ya yi a gafarta wa Shugaba Tinubu dangane da shari’ar miyagun ƙwayoyi da aka kwashe shekaru da yawa ana yi a Amurka

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Legit.ng ta lura da wasu rubututtuka a kafafen sada zumunta masu cewa mai shari’a Haruna Tsammani, shugaban kotun sauraron ƙararrakin zaben shugaban ƙasa (PEPT), ya koka ga ƴan Najeriya kan ƙin yafewa shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Magana Ta Fito: Na Kusa da Atiku Abubakar Ya Tona Asirin Gwamnatin Shugaba Tinubu Kan Abu 1 Tal

Rubutun wanda za a iya gani a nan, sun yi iƙirarin cewa mai shari’a Tsammani ya nemi jin dalilin yi da ya sa ƴan Najeriya suka kasa gafarta wa Shugaba Tinubu kan “laifin safarar miyagun ƙwayoyi” da ya yi a baya.

An yi ikirarin cewa Tsammani ya nemi yan Najeriya su yafe wa Tinubu
Babu gaskiya a batun cewa Haruna Tsammani ya nemi yan Najeriya su yafe wa Tinubu Hoto: Funmi Fayomi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Babu wata shaida Tsammani ya nemi a yafe wa Tinubu

Batun ya fara bayyana a yanar gizo ne a cikin watan Agustan 2023, wata guda kafin PEPT ta ƙi amincewa da bukatar ƴan adawa na yin watsi da nasarar da Shugaba Tinubu ya yi a zaben shugaban ƙasa na watan Fabrairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rubutun da aka yi a kafafen sada zumunta masu zargin cewa Tsammani ya nemi a yafe wa Tinubu bisa laifin safarar ƙwayoyi, za a ganinsu a nan da nan. A wasu lokatun ma bidiyo aka mayar da su.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu, Ganduje da Manyan Hafsoshin Tsaro Sun Yi Kus-Kus Kan Abu 1 a Villa, Ƙarin Bayani Ya Fito

To amma fitaccen alƙalin ya yi wannan magana? Legit.ng ta yi bincike kan hakan.

Ya gaskiyar batun yake?

Ba mu samu wani rahoto daga kafafen watsa labarai masu sahihanci cewa Tsammani ya yi wannan furuci ba.

Bayan haka, rubutun da aka yi ba su bayyana inda da kuma lokacin da alƙalin ya yi maganar ba.

Atiku Ya Yi Nasara Kan Tinubu a Kotun Amurka

A wani labarin kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP ya samu nasara a ƙarar da ya shigar a gaban kotun Amurka.

Kotun arewacin Illinois ta ƙasar Amurka ta amince da buƙatar da Atiku ya shigar gabanta ta sakin takardun karatun shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel