Har da Talauci: An Gano Abubuwa 3 da Ke Kara Yaduwar Cutar HIV

Har da Talauci: An Gano Abubuwa 3 da Ke Kara Yaduwar Cutar HIV

  • Likitoci sun danganta karuwar sababbin masu kamuwa da HIV a Najeriya da talauci, raguwar tallafin ƙasashen waje da kuma raguwar wayar da kai
  • Sun gargadi cewa matsalar kuɗaɗe na iya rusa nasarorin da aka samu wajen dakile HIV, tare da ƙara yawan masu kamuwa idan ba a ɗauki mataki ba
  • Masana sun buƙaci gwamnati ta ƙara kashe kuɗi, ta rage wariya, ta faɗaɗa gwaji da magani domin cimma burin yaƙi da HIV nan da 2030

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Likitoci sun bayyana cewa karuwar sababbin masu kamuwa da cutar HIV a Najeriya na da alaƙa da raguwar tallafin kasashen waje.

Masana harkokin lafiya sun kuma danganta haka da ƙarin talauci da kuma raguwar shirye-shiryen wayar da kai.

Likitoci sun yi magana kan yaduwar cutar kanjamau
Ministan lafiya a Najeriya, Mohammed Ali Pate. Hoto: Federal Ministry of Health.
Source: Twitter

Abubuwan da ke kara yaduwar HIV

Kara karanta wannan

Murkushe ƴan adawa da abu 3 da ƴan Najeriya ke fargaba game da ƴansandan jihohi

Sun yi gargadin cewa matsalar kuɗaɗe, talauci da raguwar wayar da kai na barazana ga nasarorin da aka samu wajen hana yaɗuwar HIV, kuma hakan na iya rusa ci gaban shekaru, cewar Punch.

Masanan sun ce raguwar tallafin ƙasashen waje ta shafi shirye-shiryen kariya da ayyukan gwajin HIV, yayin da matsin tattalin arziki ke tura mutane zuwa halayen haɗari.

Rahoton Ma'aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama'a na shekarar 2025 ya nuna cewa an samu sababbin masu kamuwa da HIV 102,025 a jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa babu maganin da ke warkar da HIV gaba ɗaya, sai dai ana amfani da magungunan rigakafin ƙwayar cutar domin dakile yaduwarta.

Najeriya na daga cikin ƙasashen da ke da mafi yawan masu ɗauke da HIV a duniya, kuma tana dogaro sosai da tallafin ƙasashen waje wajen yaƙi da cutar.

Ana samu karuwar cutar HIV a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Yadda aka rage tallafin yaki da HIV

Bayan dawowar shugaban Amurka, Donald Trump, gwamnati ta rage tallafin ƙasashen waje, ciki har da shirin PEPFAR da ke tallafawa yaƙi da HIV.

Dakatar da tallafin ya shafi gwaji, wayar da kai, ilimantarwa da shirye-shiryen tallafawa masu ɗauke da HIV a Najeriya da sauran ƙasashe.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tafka barna a Sokoto, sun kashe basarake, ɗansa da wasu mutane

UNICEF ta bayyana a watan Agustan 2025 cewa tana fuskantar gibin dala miliyan 160 wajen gudanar da ayyukan jin ƙai a Najeriya, cewar Daily Post.

Matsalar kuɗaɗen ta sa asibitoci da dama suka rasa kayan gwajin HIV, yayin da masu fama da cutar suka koka kan rage yawan magungunan da ake ba su.

Ko da yake gwamnatin tarayya ta amince da kashe naira biliyan 4.8 domin sayen fakitin magungunan HIV 150,000 tare da ware dala miliyan 200, har yanzu ana fuskantar ƙalubale.

Masanin tarin fuka da HIV, Dakta Dan Onwujekwe, ya danganta karuwar masu kamuwa da HIV da ƙarin talauci a fadin Najeriya.

Ya ce talauci na sa mutane zuwa cibiyoyin lafiya marasa rajista, inda ake amfani da kayan aiki marasa tsafta da ka iya haifar da kamuwa da cututtuka.

An fara riga kafin cutar HIV

An ji cewa Gwamnatin Anambra ta fara amfani da maganin LEN PrEP domin dakile yaduwar cutar HIV musamman tsakanin masu hadarin kamuwa da ita.

Ana yin sabuwar allurar rigakafin cutar kanjamau (HIV) sau biyu kacal a shekara sabanin magungunan da ake sha kullum don yaki da cutar.

Jihar Anambra na da 2.4% na masu dauke da HIV, mafi yawa a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, kamar yadda rahoto ya nuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com