Rana Zafi, Inuwa Kuna: Ana Fargabar 'Yan Gudun Hijira 500 Sun Nutse a Teku

Rana Zafi, Inuwa Kuna: Ana Fargabar 'Yan Gudun Hijira 500 Sun Nutse a Teku

  • Jiragen ruwa biyu da suka ɗauki fiye da 'yan gudun hijirar Rohingya 500 sun bace a teku bayan sun tashi daga jihar Rakhine ta Myanmar
  • Masana na zargin jiragen sun nutse sakamakon mummunar guguwar damina, yayin da babu wani tabbataccen rahoto kan waɗanda suka tsira
  • Rikicin da ake fama da shi a Myanmar da kuma fatan samun mafaka a Malaysia ne suka tilasta wa dubban 'yan Rohingya shiga jirgin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Myanmar – Ana fargabar cewa fiye da 'yan gudun hijirar Rohingya 500 sun rasa rayukansu bayan wasu jiragen ruwa biyu da suka ɗauke su sun bace a teku tun bayan tashinsu daga jihar Rakhine ta ƙasar Myanmar.

Rahotanni sun nuna cewa jiragen biyu sun ɗauki kimanin mutane 530, amma tun bayan tashinsu ba a sake jin wani labari daga gare su ba.

Kara karanta wannan

Sojojin Amurka da dama sun jikkata bayan hare haren da Iran ta kai masu

Jirgi na tafiya a teku
Wasu mutane na tuka jirgin ruwa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

BBC ta wallafa cewa akwai yiwuwar jiragen sun nutse saboda lokacin damina ya fara, lamarin da ya haddasa tashin manyan igiyoyin ruwa, yayin da jiragen da ake amfani da su tsofaffin jiragen kamun kifi ne da aka canza domin ɗaukar fasinjoji.

Ana zargin duk sun nutse

Masu bibiyar lamarin sun bayyana cewa da alama kaɗan ne ko kuma babu wanda ya tsira daga hatsarin, inda aka kiyasta cewa rabin fasinjojin mata da yara ne.

Shugabar ƙungiyar Arakan Project, Chris Lewa, ta ce ta yi ƙoƙarin gano abin da ya faru, amma rikicin da ake fama da shi a Rakhine ya sa sadarwa ta kusan ɗaukewa gaba ɗaya.

Ta ce bayan kusan makonni uku da tashin jiragen, iyalan fasinjojin ba su samu wani saƙo daga gare su ba, abin da ya ƙara tabbatar da fargabar cewa jiragen sun nutse.

Hukumomin Bangladesh sun gano gawar wata mata da ruwa ya fito da ita bakin teku, yayin da wasu masunta suka gano ƙarin gawarwaki a tsakanin yankin Irrawaddy Delta da gabar jihar Mon.

Kara karanta wannan

An yi kicibis, sojoji sun yi ram da 'dan bindiga a hanyar sintiri

Me yake faruwa a Rohingya?

A halin yanzu sama da 'yan Rohingya miliyan daya na zaune a sansanonin 'yan gudun hijira a Bangladesh, inda suke fama da ƙarancin tallafi, rashin aikin yi da kuma matsalolin tsaro.

Sauran kusan mutum 600,000 da ke cikin jihar Rakhine suna rayuwa cikin mawuyacin hali sakamakon yaƙi tsakanin sojojin Myanmar da ƙungiyar Arakan.

Min Aung Hlaing
Shugaban Myammar, Min Aung Hlaing. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

UN News ta wallafa cewa saboda wannan hali, dubban Rohingyawa na ƙoƙarin tserewa zuwa Malaysia, inda ake da al'ummar Rohingya kusan 200,000.

Lamarin ya haifar da bunƙasar safarar mutane ba bisa ƙa'ida ba, inda masu safarar ke karɓar kusan dala 3,000 daga kowane mutum domin kai shi Malaysia ta Myanmar, Thailand da sauran ƙasashe.

NCAA ta dakatar da matukin jirgi

A wani labarin, mun ruwaito cewa Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta dakatar da matukin jirgin da ke da alhakin hatsarin da ya faru a filin jirgin saman Asaba.

Kara karanta wannan

Mutane sun kone kurmus da motar gas ta fashe a kusa da sojoji

Shugaban NCAA, Kyaftin Chris Najomo, ya ce an kuma dakatar da mataimakin matukin jirgin da kamfanin da ke sarrafa jirgin har sai an kammala bincike kan lamarin.

Ya ƙara da cewa duk da cewa Hukumar Binciken Hatsurran Sufurin Najeriya (NSIB) ce ke jagorantar binciken, NCAA ma ta fara nata binciken domin gano ko an karya dokokin sufurin jiragen sama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng