Wasu sarakunan yankin Yarbawa na aiki tare da makiyaya da ke garkuwa, Sanata Fadahunsi
- Sanata Francis Fadahunsi daga jihar Osun ya yi ikirarin cewa wasu sarakunan yankin na hada kai da makiyaya don aikata laifuka
- Sanatan ya kuma ce makiyaya Fulani da ke aikata laifuka a yankin baki ne da suke hada baki da sarakuna
- Sanata Fadahunsi ya ce sun dade suna zamansu lafiya tsawon shekaru fiye da 100 da makiyaya Fulani ba tare da matsala ba
Mataimakin kwamitin majalisar dattawa na Kwastam, Sanata Francis Fadahunsi na jam'iyyar PDP daga Osun East ya ce akwai wasu masu sarautar gargajiya a Kudu maso Yamma da ke tare da makiyaya don aikata muggan ayyuka a yankin, Vanguard ta ruwaito.
A cewarsa, makiyaya da suka hada kai da wasu masu sarautun gargajiya a kudu maso yamma ne ke aikata garkuwa, fyade, fashi, kashe-kashe da lalata dukiyoyi da ma wasu miyagun ayyuka.
DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace fasinjoji 18 ciki har da abokan ango a Niger
Sanatan, wanda tsohon jami'in kwastam ne, ya koka kan yadda wasu masu sarautun gargajiyan ke taimakawa wurin aikata laifuka inda ya ce an dade ana fama da rashin tsaro a yankin.
Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a ranar Litinin a Abuja kan korar makiyaya da wasu gwamnonin Kudu maso Yamma suka yi, dan majalisar ya ce, "Fulani daga kasashen ketare ne suke garkuwa da mutane amma suna samun taimako daga wasu Sarakuna da ke amfani da su."
KU KARANTA: Babu wanda ya isa ya kore mu daga yankin kudu maso yamma, in ji Miyetti Allah
Sanatan ya ce sun dade suna rayuwa da Fulani a yankinsu tsawon shekaru 100 da suka shude kuma ba su kashe su don haka baki ne ke aikata laifukan.
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.
Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng