1943-1998: Tarihin rayuwa da mulkin Marigayi Janar Sani Abacha a Najeriya

1943-1998: Tarihin rayuwa da mulkin Marigayi Janar Sani Abacha a Najeriya

A rana irin ta yau a shekarar 1998 aka wayi gari da rasuwar shugaban kasa Janar Sani Abacha a Najeriya. Abacha mai shekaru 54 ya shafe shekaru kusan biyar ya na mulkin soji.

Yayin da aka cika shekaru 22 da rasuwar shugaban kasar, mun kawo kadan daga cikin labarinsa:

1. Janar

Sani Abacha ne Sojan farko a tarihi da ya zama cikakken Janar ba tare da ya yi tsallaken matsayi ba. Abacha ya shafe shekaru 35 a gidan soja kafin ya samu wannan matsayi.

2. Juyin mulki

Ana tunanin cewa Sani Abacha ya na da hannu a kusan duka juyin mulkin da aka yi a Najeriya. Da shi aka hambarar da gwamnatoci a 1966, 1975, 1983, da 1985 kafin ya hau mulki.

3. Rashin magana

Janar Sani Abacha mutum ne maras magana, don haka ne ma manyan sojojin kasar su ka rasa gane kan gabansa. A lokacin da Abacha ya yi mulki, bai cika magana da ‘yan jarida ba.

KU KARANTA: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka da zarar an wallafa

4. Hawa shugaban kasa

A karshen 1993 ne Janar Sani Abacha ya hambarar da gwamnatin wucin-gadin Ernest Shonekan. Abacha ya kifar da Shonekan daga mulki ne ba tare da an kashe ko kyankyaso a kasar ba.

5. Gwamnati

Gwamnatin Sani Abacha ta ragewa Najeriya bashin da ke kanta da kusan Dala biliyan 10. Haka zalika Abacha ya bunkasa asusun kudin kasar wajen Najeriya zuwa fam Dala biliyan 9.6

Gwamnatin Abacha ta gina tituna a manyan biranen Najeriya irinsu Kano, Gusau, Benin, Funtua, Zaria, Enugu, Kaduna, Aba, Legas, Lokoja da Fatakwal. Sannan ya kafa hukumar PTF.

6. Fada da ‘Yan tawaye da kasashe

Sani Abacha ya samu kansa cikin sabani da ‘yan tawayen gida da tsofaffin sojojin da ya kama da zargin juyin mulki. Abacha ya yi fada da kasashen Duniya a dalilin irin salon mulkinsa.

7. Mutuwa

Janar Abacha ya mutu ne kwatsam cikin wani hali mai ban mamaki a fadar shugaban kasa. A wannan rana aka wuce da gawarsa zuwa mahaifarsa ta Kano inda aka yi masa jana’iza.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel