Daura ta Cika ta Batse da Jiga-Jigan 'Yan Siyasa da Boko Yayin da Tsohon DG DSS ke Aurar da Diya

Daura ta Cika ta Batse da Jiga-Jigan 'Yan Siyasa da Boko Yayin da Tsohon DG DSS ke Aurar da Diya

  • Garin Daura ya cika dankam sakamakon daurin auren diya tsohon DG na hukumar DSS, Alhaji Lawal Daura
  • Daga cikin manyan bakin da suka halarta akwai, Abdurrahman Dambazau, Sanata Yusuf Yusuf, Mataimakin gwamnan Katsina da sauransu
  • An daura auren kan sadaki N100,000 kuma ango ya sanar da cewa 'yar uwarsa ce ta hada shi da amaryar saboda Landan yake zama

Daura, Katsina - Daura, garinsu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika ya batse yayin da tsohon darakta janar na hukumar tsaron farin kaya, DSS, Alhaji Lawal Musa Daura, ya aurar da diyarsa.

Lawal ya aurar da kyakyawar diyarsa ga masoyinta, haifaffen garin Gusau, Injiniya Abdullahi Lawal Abba a garin Daura a ranar Juma'a, Daily Trust ta rahoto.

Lawal Daura
Daura ta Cika ta Batse da Jiga-Jigan 'Yan Siyasa da Boko Yayin da Tsohon DG DSS ke Aurar da Diya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Babban Limami Sheikh Abdulkadir Ibrahim ne ya daura auren da aka yi a masallacin Low Cost dake Daura.

Kara karanta wannan

Bidiyoyin: Yadda Matasa Suka Yi Ruwan Liki Harda Su Daloli A Wajen Shagalin Dinan Dan Sarkin Kano

Jiga-jigai daga sassan kasar nan da suka hada da tsohon shugaban rundunar sojin kasan Najeriya, Laftanal Janar Abdurrahman Dambazau ya samu halarta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran sun hada da Sanata Yusuf Yusuf daga taraba, Sanata Abdullahi Gumel daga Jigawa, mataimakin shugaban hukumar gidajen gyaran halin, Alhaji Lawal Abdullahi.

Hakazalika, mataimakin gwamnan jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Faskari, kwamishinan kananan hukumomi Alhaji Ya'u Gwajo-gwajo, magajin Daura da Alhaji Musa Daura duk sun samu halarta.

Ango ya biya sadaki N100,000 inda daga nan aka daura auren a masallacin.

A yayin jawabi ga manema labarai bayan daura auren, angon wanda Injiniyan tsaro ne kuma mazaunin Landan, yace 'yar uwar shi ce ta hada auren yayin da baya kasar.

"Ina Landan lokacin da 'yar uwata ta hada mu bayan ta gamsu da dabi'unta tare da tarbiyyarta. Daga waya daya na fada soyayyarta duk da ban taba ganinta ba. Ina matukar farin ciki da hukuncin da na yanke," yace.

Kara karanta wannan

Hotuna: An Bude Katafaren Masallacin Kaltungo, jihar Gombe Ranar Juma’a

A jawabinsa, mahaifin amarya Lawal Daura, ya mika godiya ga Allah kan abinda ya kira da taro mai ban sha'awa kuma ya mika godiyarsa ga duka wadanda suka halarta.

"Kamar kodayaushe, ina fatan zaman lafiya tsakanin ma'auratan tare da mika gdoiya ga wadanda suka hallara. Abokai, 'yan uwa da duk wanda ya samu damar zuwa," yace.

Daura yayi addu'ar zaman lafiya da daidaito a kasar nan. An yi liyafa ga bakin da suka halarci wurin a Daura Motel.

Bidiyon Shigowar Kasaita da Iyalan Bayero Suka yi Wurin Liyafar Auren Kabiru Aminu Bayero

A wani labari na daban, ana cigaba da shagalin auren Kabiru Aminu Ado Bayero da kyakyawar amaryarsa Aisha Ummarun Kwabo a garin Sokoto.

Tun daga fara shagalin bikin garin Sokoto ya dauka 'yan uwa, masoya da abokan arzikin ango Kabiru Aminu Bayero da amaryarsa Aisha Ummaru Kwabo.

Bayan shagalin kamun amarya Aisha da aka yi a daren Laraba, daren Alhamis an yi liyafar cin abincin dare inda aka ga kwai da kwarkwatar iyalan Bayero a wurin kasaitacciyar liyafar.

Kara karanta wannan

Allah Yayi wa Tukur Othman, Tsohon Manajan Daraktan Jaridar New Nigerian, Rasuwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel