Trump Ya Gamu da Cikas a Kotu kan Yunkurin Abin da Yake Son Yi a Amurka

Trump Ya Gamu da Cikas a Kotu kan Yunkurin Abin da Yake Son Yi a Amurka

  • Wata alƙalin kotun tarayya a Amurka ta dakatar da sabon yunƙurin Shugaba Donald Trump na hana wasu yaran da aka haifa a ƙasar samun zama ’yan ƙasa kai tsaye
  • Kotun Ƙoli ta Amurka ta riga ta tabbatar cewa kundin tsarin mulkin ƙasar na ba yaran da aka haifa a Amurka damar zama ’yan ƙasa
  • Mai shari'a Deborah Boardman ta ce sabon umarnin Trump kusan tabbas ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Amurka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Wata alƙalin kotun tarayya a Amurka ta dakatar na ɗan lokaci da sabon yunƙurin Shugaba Donald Trump na takaita dokar samun zama ɗan ƙasa ta hanyar haihuwa.

A watan Yuni, Kotun Ƙoli ta Amurka ta soke wani umarnin zartarwa da Trump ya gabatar a ranar farko da ya koma ofis, wanda ke neman takaita wannan damar.

Kara karanta wannan

Da hannun gwamnatin Najeriya a yunkurin juyin mulki a Nijar? An gano gaskiya

Shugaba Donald Trump ya gamu da cikas a kotu
Shugaba Donald Trump a wajen taron G-7 Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kotun ta yanke hukunci da ƙuri’u 6-3 cewa kundin tsarin mulkin Amurka ya ba yaran da aka haifa a ƙasar damar zama ’yan ƙasa tun daga haihuwa, cewar rahoton tashar NBC News.

Hakan ya haɗa da yaran da iyayensu ba su da takardun izinin zama a Amurka ko kuma waɗanda ke zaune a ƙasar na ɗan lokaci.

Trump ya zartar da wasu dokoki

Sai dai a watan da ya gabata, Trump ya sanya hannu kan wasu sabbin umarnin zartarwa guda biyu da ke neman ƙara takaita damar samun zama ɗan ƙasa ta hanyar haihuwa.

Sabbin umarnin ba su tsaya kan yaran baƙin haure da suka shiga Amurka ba bisa ƙa’ida ba kawai ba.

Sun kuma shafi yaran ma’aikatan ƙasashen waje da ke Amurka bisa ƙa’ida, ciki har da ma’aikatan ofisoshin jakadanci da ma’aikatan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa kamar Majalisar Ɗinkin Duniya da Bankin Duniya.

Lauyoyi sun garzaya kotu

Kara karanta wannan

Hanyar da Argentina za ta karrama Messi bayan ritaya daga taka mata leda

Bayan fitar da umarnin, wasu baƙin haure da lauyoyinsu sun ƙalubalanci matakin gwamnatin Trump a kotu.

A ranar Laraba, Alƙaliya Deborah Boardman ta bayar da umarnin wucin gadi na dakatar da aiwatar da sababbin dokokin.

Ta ce akwai yiwuwar umarnin ya saɓa wa haƙƙin da kundin tsarin mulkin Amurka ya tanada na bai wa mutanen da aka haifa a ƙasar damar samun zama ’yan ƙasa kai tsaye.

Mai shari'ar ta ce umarnin ya saba wa kundin tsarin mulki

Boardman ta bayyana cewa umarnin Trump “kusan babu shakka ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Amurka.”

Ta ce za a ci gaba da dakatar da aiwatar da umarnin har sai an kammala shari’ar da ƙungiyoyin kare haƙƙin baƙin haure suka shigar.

"Wannan kotu dole ne, a karo na biyu, ta dakatar da aiwatar da sabon yunƙurin shugaban ƙasa na ƙwace haƙƙin zama ɗan ƙasa daga gare su.”
Kotu ta dakatar da umarnin Trump
Shugaba Donald Trump a fadar White House Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gwamnatin Trump za ta iya ɗaukaka ƙara

Ana sa ran gwamnatin Trump za ta iya ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun. Wannan ba shi ne karo na farko da mai shari'a Boardman ta dakatar da irin wannan yunƙuri ba.

Kara karanta wannan

An samu kasar da ta yanke hulda da Iran ana tsaka da yaki da Amurka

A watan Fabrairun 2025, ta riga ta dakatar da wani makamancin umarnin zartarwa da Trump ya gabatar domin kawo ƙarshen damar samun zama ɗan ƙasa ta hanyar haihuwa a Amurka.

Trump na shawarar sauya sunan Hormuz

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya ba da shawarar sauya sunan mashigar Hormuz zuwa “Trump Strait”.

Shugaba Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake ikirarin cewa Amurka ta samu cikakken iko kan mashigar Hormuz.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng