Gaskiya Ta Fito kan Labarin da Ya Nuna Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump Ya Mutu

Gaskiya Ta Fito kan Labarin da Ya Nuna Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump Ya Mutu

  • Fadar White House ta tabbatar da cewa shugaban Amurka Donald Trump yana raye bayan yaduwar jita-jita a kafafen sada zumunta
  • Jita-jitar ta samo asali ne bayan sanarwar cewa mataimakin shugaban kasar Amurka, JD Vance zai yi wa manema labarai bayani
  • Fadar White House ta ce gwajin lafiya ya nuna Trump na fama da wata matsalar da ba ta da hatsari ga rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

United States - Fadar White House ta tabbatar da cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, yana raye bayan wata jita-jita da ta yadu a kafafen sada zumunta cews ya mutu.

Jita-jitar ta bazu ne bayan wani sanarwa da fadar Shugaban Amurka watau White House ta fitar cewa mataimakin shugaban kasa, JD Vance, zai gudanar da taron manema labarai maimakon Trump.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Fadar shugaban kasa ta fadi dalilin hana fitar da bayanan Tinubu na Amurka

Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yayin da yake zantawa da manema labarai a Fadar White House Hoto: Donald J. Trump
Source: Getty Images

Sanarwar da Ofishin Yada Labarai na White House ya wallafa a shafin X ta ce:

"Mataimakin shugaban kasa @JDVance zai gabatar da bayani ga manema labarai gobe da karfe 1:00 na rana."

Yadda aka yada labarin mutuwar Trump

Wannan ne karo na farko da Vance zai gudanar da irin wannan taro tun watan Yuli, amma ba a bayyana batun da zai tattauna ba.

Haka kuma sanarwar ba ta nuna cewa akwai wani lamari na gaggawa ko matsalar lafiya da qta shafi Trump ba.

Sai dai rashin bayyana dalilin taron ya sa wasu masu amfani da kafafen sada zumunta suka fara yada jita-jitar cewa shugaban kasar ya mutu.

Cikin mintuna kadan, mutane da dama sun fara wallafa sakonni daban-daban suna ikirarin cewa Trump ya mutu, duk da babu wata shaida da ta tabbatar da hakan.

Da gaske Shugaba Trump ya mutu?

Sai dai fadar White House ta fito ta karyata wannan labari, tana mai tabbatar da cewa Shugaba Trump yana nan a raye, kamar yadda jaridar IB Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shirin cire Tinubu a mulki: Jam'iyyar PDP ta fadi matsayarta kan hadaka a 2027

A cikin watannin baya-bayan nan, an kara mayar da hankali kan lafiyar Trump bayan wasu hotuna sun nuna wasu alamomi a hannunsa na dama da kuma kumburi a kafafunsa.

Tambayoyi kan lafiyarsa sun kara yawa yayin da yake kai ziyara zuwa asibitin sojoji ta Walter Reed National Military Medical Center.

Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald Trump
Source: Getty Images

Trump ya koma Fadar White House a watan Janairun 2025 bayan lashe zaben shugaban kasar Amurka na 2024.

Yana da shekara 80 a duniya kuma zai ci gaba da rike mukamin shugaban kasa har zuwa watan Janairun 2029 idan ya kammala wa'adinsa na biyu.

Shekarunsa sun sanya jama'a da kafafen yada labarai kara bibiyar lafiyarsa, musamman bayan ganin wasu canje-canje a jikinsa a hotuna.

Trump na son sauya sunan Hormuz

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Donald Trump ya ba da shawarar sauya sunan mashigar Hormuz zuwa “Trump Strait”, yana mai cewa yanzu Amurka ce ke da cikakken iko a mashigar.

Fadar White House ta wallafa taswirar mashigar tare da sabon sunan da Trump ya bayar, yayin da ake ci gaba da yaki tsakanin Amurka da kasar Musulunci ta Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262